ƘUDIRIN PIB: Majalisa ta yi biris da ƙorafen-ƙorafen gwamnonin kudu, ta miƙa wa Buhari ya sa hannu kawai – Akpabio

0

Ministan Harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya shawarci Majalisar Dattawa cewa ta daina tsayawa sauraren ƙorafe-ƙorafen jama’a a kan Kudirin Dokar Raba Ribar Fetur, ta miƙa wa Shugaba Buhari gyaran da su ka yi, shi kuma ya sa hannu ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya ce a daina tsayawa sauraren bimbinin al’ummar yankin da ake haƙo fetur, a saki dokar kawai ta fara aiki, a wuce wurin.

Idan ba a manta ba, Dattijo kuma jagoran Yankin Neja Delta Edwin Clerk, ya yi barazanar cewa za su hana haƙo ɗanyen mai a Najeriya saboda ƙudirin dokar ribar fetur ta fifita wasu jihohin Arewa kan jihohin da ake haƙo mai.

Dattijo mai faɗa a ji a yankin Neja Delta, ya bayyana cewa za su hana kamfanonin haƙo ɗanyen mai su ci gaba da aiki a yankin Neja Delta, matsawar dai ba a dawo da kudirin raba ribar man fetur da Majalisa za ta gabatar ba.

Clerk ya ce ‘Yan Majalisar Dattawa da na Tarayya sun raina wa al’ummar Yankin Neja Delta wayau, saboda sun soke kason kashi 10 bisa 100 da za a riƙa ba Neja Delta, su ka maida shi kashi 3 bisa 100, sannan su ka lafta wa wasu jihohin Arewa har kashi 30 bisa 100.

Ya kira wannan ƙudiri da cewa, ƙudirin iya shege ne da shaiɗanci da kuma tantagaryar rashin adalci.

“Lokacin Daina Yi Mana Mulkin Mallaka Ya Yi” -Edwin Clerk

“Mu na gargaɗin cewa jama’ar Neja Delta da an kai su bango. Tutar ta isa haka. Mun gaji da irin mulkin da ake yi mana mai kama da mulkin mallaka, wanda ‘yan uwan mu da abokan mu ‘yan Arewa ke yi mana.

“A yau ragamar harkokin fetur a ƙasar nan ta na hannun ‘yan Arewa, duk da dai harkokin yaƙi man kamfanonin ƙasashen Turai ne ke gudanarwa a madadin Gwamnatin Tarayya.” Inji Clerk.

Dattijo Clerk wanda shi ne jagoran wata ƙungiyar kare muradun Neja Delta, PANDEF, ya ce shi da sauran ɗaukacin dukkan ‘yan Neja Delta sun ƙi amincewa da kason cikin cokali na kashi 3 bisa 100 na ribar mai da za a ba yankin Neja Delta sa kuma kashi 5 cikin 100 da aka ware wa NNPC Limited da za a rika bai wa al’ummar yankin da ake haƙo man.

“Idan ba a yi mana haka ba kuwa, to ya zama tilas mu tashi tsaye mu fito mu ƙwaci haƙƙin mu da tsiya-tsiya. Kuma sai mu hana kamfanonin haƙo ɗanyen mai ci gaba da aikin haƙar mai a yankin mu.”

Shi kuwa Akpabio cewa ya yi “wannan ƙudiri da tun shekaru 20 ya ke jibge a Majalisar Tarayya da ta Dattawa. Ina magana ne a madadin jama’ar Neja Delta. Kada fa su jangwalo abin da zai ƙara kawo wa wannan ƙudiri cikas. Ko kashi nawa za a ba mu, ko 3, 4 ko biyar kawai mu haƙura mu karɓa. Daga baya mu koma mu nemi ƙari.”

Share.

game da Author