Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa Hukumar Abinci ta Duniya ta yi gargaɗin cewa al’ummar Arewacin Najeriya za su fuskanci gagarimar matsalar ƙarancin abinci.
Majalisar, da kuma Hukumar FAO sun ƙiyasta cewa aƙalla mutum miliyan 13 ne za su kasa zaune su kasa tsaye saboda ƙarancin abinci a Arewacin Najeriya.
Manajan Ayyuka na Hukumar UNDP-GEF, wanda shi ne ke kula Ayyukan Bunƙasa Abinci Afrika, mai suna Rhoda Dia, shi ne ya yi wannan bayani a ranar Laraba, yayin da ya ke magana da manema labarai a Abuja.
Sai ta yi hira ta wayar tarho cewa ƙarancin abincin zai shafi Arewacin Najeriya saboda tsawon shekaru sama da 12 da aka shafe ana tashe-tashen hankula.
Ta ce tuni dama ƙarin matsalolin rashin tsaro a Arewa sun daɗa haifar da fatara, talauci da ƙuncin rayuwa a yankin Arewa.
Dia ta ce to kuma sai ɓullar cutar korona ta ƙasa sa waɗannan matsaloli su ka ƙara ta’azzara. Ga kuma rikice-rikice na makiyaya da manoma da hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane su na karɓar kuɗaɗen fansa, abin da ya ƙara haifar da ƙuncin rayuwar.
Ta ce mata, ‘yan mata da ƙananan yara su ne lamarin ya fi shafa sai kuma dattawa marasa ƙarfin tashi su nema.
PREMIUM TIMES Hausa ta lura da yadda ɗimbin mutanen karkara ke ta hijira daga ƙauyukan su a wasu jihohin ƙasar nan, musamman daga Katsina su na komawa cikin Kano, inda a yanzu shi ne birnin da marasa galihu ke cincirindo a ciki su na barace-barace da sauran sana’o’in da lallai ba ne su iya riƙe mutum.