ZAZZABIN LASSA: Mutum 292 sun kamu, 59 sun mutu a Najeriya

0

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 292 sun kamu da zazzabin Lassa a Najeriya.

NCDC ta Kara da ce adadin yawan mutanen da suka mutu a dalilin cutar sun kai 59 bayan mutum daya din da aka samu a jihar Ondo a mako na 22.

Mutum 25 sun mutu a jihar Ondo, Edo-14, Taraba -11, Ebonyi- 2, Bauchi-2, Kaduna- 4 da Enugu- 1.

Hukumar NCDC ta ce tsakanin mako na 16 da mako 22 mutum 9 sun mutu.

“A mako na 16 mutum daya ya mutu a jihar Edo, mutum daya a jihar Ondo.

“A mako na 17 mutum biyu sun mutu a jihar Ondo, daya a jihar Ebonyi.

“Mako na 19 mutum daya kawai ya mutu a jihar Ondo.

Hukumar ta ce mutum 292 ne suka kamu a jihohi 14 da kananan hukumomi 57 a kasar nan.

Har zuwa yanzu jihohin Edo da Ondo ne suka fi fama da yaduwar cutar a Najeriya.

Dalilin da ya sa mutane ke mutuwa a dalilin kamuwa da zazzabin lassa.

Jami’in gudanar da bincike kan cututtuka na jihar Ondo Stephen Fagbemi ya ce talauci na daga cikin dalilan dake sam mutane mutuwa idan suka kamu da cutar.

Fagbemi ya Kuma ce har yanzu akwai mutanen dake cewa wannan zazzabi na lassa asiri ne kawai wata tsafi ne shi ya sa da zaran mutum ya kamu sai a garzaya gidanen bokaye.

Matakan Kiyaye Kamuwa Da Zazzabin Lassa

1 – A raba beraye da shiga cikin gida: Kada a yi sakaci har beraye su samu wurin zama a cikin gida.

2 – A toshe duk wani rami a gida: Beraye daga wani gida kan shigo maka su boye, idan ka bar ramu a cikin gidan ka.

3 – A rika barin abinci ya dahu sosai: A rika cin abin da aka dafa ya dafu sosai.

4 – A guji taba mataccen bera ko mai rai da hannu: Taba mataccen bera ko mai rai da hannu na iya sa a kamu da cutar Zazabin Lassa.

5 – A rika yawaita tsaftace gida da kewayen sa: Barin datti a gina na kawo beraye ko daga waje ko daga wani gida.

6 – Kada a ci kayan marmarin da bera ya saka baki a kai: Wannan ganganci ne sosai, don haka a guji ci ko da kuwa an wanke.

7 – A rika ajiye abinci a wuri mai murfi: Bri abinci a bude kan kai bera ya ci, kuma har yayi fitsari ko kashi a kai.

8 – A rika rufe kwandon zuba shara: Beraye na buruntu cikin kwandon shara, su na cin sauran abincin da aka zubar.

9 – A rika wanke hannu da sabulu da ruwa mai tsafta: Dama wannan na cikin matakan farko na tabbatar da tsafta a jikin mutum.

10 – A rika garzayawa asibiti idan babu lafiya: Garzayawa asibiti ya fi a tsaya ana kame-kamen shan magani a gida.

11 – A daina shanya abinci a waje kuma a bude a kasa: Barin abinci a bude illa ce, sannan shanya abinci a kasa ko a kan dabe kan haifar da cututtuka.

12 – A guje kusantar wanda ya kamu da cutar: Likita ne kadai zai iya kusantar wanda ya kamu da zazzabin lassa. Don haka a kiyaye.

Share.

game da Author