Zan maida hankali wajen inganta rayuwar sojojin Najeriya – Janar Faruk, BHSN

0

Sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Manjo Janar Faruk Yahaya, ya sha alwashin inganta rayuwar sojojin Najeriya, tare da ƙara himma wajen ganin sun ƙara samun ƙwarewa da kuma yin sakayya ga waɗanda su ka yi rawar gani.

Ya ce zai yi waɗannan tare da yin aiki tuƙuru, aiki da gaskiya da kuma tafiyar da komai a cikin tsentseni.

Ya yi wannan alƙawarin ne a zaman ganawar sa ta farko da manyan jami’an sojoji da kwamandoni a ranar Litinin a Abuja.

An naɗa Manjo Janar Yahaya a ranar 22 Ga Mayu, bayan rasuwar Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama, a Kaduna.

Yahaya ya ce nauyin da ke wuyan sojojin Najeriya gagarimi ne, sai ya ƙara yin kira ga ɗaukacin sojojin Najeriya su ƙara tashi tsaye haiƙan wajen kare ƙasar nan.

Ya kuma yi alƙawarin gudanar da mulki wanda zai zama nagari abin koyi a bisa tsarin da hukumar sojojin Najeriya ta shimfiɗa.

Sannan ya yi alƙawarin maida rundunar sojojin Najeriya mashahuriya kuma ƙaƙƙarfa, yadda za ta zama mai ƙarfin kare ƙasar nan daga dukkan wata barazanar tsaron da ta taso a Najeriya.

Ya ce idan rundunar sojojin Najeriya na so ta riƙa gogayya da takwarorin ta na wasu ƙasashe, to tilas sai an ƙara himma wajen bijiro da ayyukan ƙara himma wajen cusa ƙwarewa a aikin sojoji.

Daga nan ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari alƙawarin biyayya da kuma rantsuwar kare ƙasar nan daga hare-hare ko wata barazana ta ciki da wajen Najeriya.

Share.

game da Author