Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya dakatar da Sarkin Zurmi, Atiku Abubakar, bayan an zarge shi da ko-in-kula yayin da ‘yan bindiga su ka kashe mutum 61 a masarautar sa.
A ranar Juma’a waccan ce mahara su ka kashe mutum 61 a ƙauyukan Zurmi a wani mummunan hare-haren da su ka kai.
Maharan waɗanda su ka riƙa farmaki a kan babura, sun riƙa kashe mutane ba ji ba gani, baya ga waɗanda su ka ji raunuka da kuma maza da mata da yara waɗanda su ka gudu su ka bar ƙauyukan su.
Gwamna ya naɗa Bello Suleiman mai riƙe da sarautar Bunun Kanwa ya riƙe Masarautar Zurmi kafin Kwamitin Binciken Sarki ya bada rahoton binciken zargin da aka ce ake wa sarkin.
A wancan makon ne hasalallun mutane daga ƙauyuka su ka yi zanga-zanga a cikin Zurmi inda har su ka banka wa wani sashen Fadar Sarki wuta.
“Mun tattara gawarwakin mutane 51, daga baya kuma aka gano wasu gawarwakin 10.” Haka majiyar da ta nemi wakilin mu ya ɓoye sunan sa ya bayyana.
Kuma ya ce a kan babura aka riƙa kai masu hare-haren da rana ƙiri-ƙiri.
Mazauna ƙauyukan dai sun zargi jami’an tsaro da Sarkin Zurmi da kasa yin wani kataɓus wajen ƙoƙarin kai masu ɗauki.
Sau da dama dai ana zargin masu riƙe da Sarautun Gargajiya na haɗin-baki da masu garkuwa.
Cikin watan Mayu ne Masarautar Katsina ta tsige Hakimin Ƙanƙara, bayan kwamitin bincike ya same shi da hannu wajen mu’amala da ‘yan bindiga.