ZAFTARE MA’AIKATAN KADUNA: Ƙungiyar kwadago za ta dawo Kaduna yin zanga-zangar da ya fi na baya

0

Kungiyar kwadago ta kasa ta bayyana cewa da zarar ta kammala shirinta za ta diri garin Kaduna domin gudanar da zanga-zangar da ya fi wanda ta yi a baya a jihar.

Kungiyar ta ce gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya ki cika alkawuran da ya ɗauka na dakatar da zaftare ma’aikatan jihar.

Ayuba Wabba, shugaban kungiyar ya ce gwamna El-Rufai ya ki barin abinda ya ƙudiri kuma suma fa ba za su fasa abin da suke shirya wa ba.

” Muna nan muna aiaikawa da wasiku zuwa rassan kungiyoyin ma’aikata cewa su shirya su kuma fara sanarwa ma’aikata cewa su fara kimtsawa da shiri domin za a dira Kaduna, kuma wannan karon za ayi ta ne ta kare ne.

” Mun rubuta wa shugaban kasa wasika, mun yi wa ministan kwadago shima cewa El-Rufai ya ki cika alkawarin da ya dauka, ya na nan yana korar ma’aikata. Saboda haka za mu dawo Kaduna zanga-zanga har sai ya bi yarjejeniyar da aka yi.

Sai dai kuma El-Rufai ya ce shima fa a wannan karon ya shirya wa kungiyar Kwadagon. Kuma yayi musu barazanar idan sun isa su dawo Kaduna su gani.

” Mun sani kuɗi ake basu daga Abuja su zo su yi mana rashin mutunci a Kaduna, wannan karon muma a shirye muke, idan sun isa su dawo Kaduna da sunan zanga-zanga, za su ko sha mamaki.

Share.

game da Author