Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa yoyon da wani ɓangaren ginin Majalisar Dattawa ke yi, hujja mai nuna cewa ginin ya na buƙatar a yi masa kwaskwarima.
Lawan ya ce danƙareren ginin Majalisa na ɗaukacin jama’ar ƙasar nan ne baki ɗaya su, don haka gyara shi abu ne mai muhimmanci matuƙar gaske.
Shugaban ya yi wannan bayani ne a yau Laraba, lokacin da zai fara jawabi a zaman majalisa na ranar Laraba.
Lawan ya yi wannan bayani ne da Mataimakin Bulalar Majalisa, Sabi Abdullahi ya yi wani ƙorafi dangane da rahoton da ya ce gidan talabijin na Channels ya yi, kan yoyon da ruwan sama ya riƙa yi a rufin Majalisa, ranar Talata.
Sabi ya nuna cewa rahoton ya sosa masa rai, kuma an keta masa irli da mutunci a matsayin sa na sanata.
Sauran wuraren da su ka riƙa yoyon ruwan sama, har da Dandalin ‘Yan Jarida, inda su ke zama su na ɗaukar labaran yadda zaman majalisa ke wakana.
Wuraren sun riƙa zubar ruwa ne duk kuwa da ɗimbin biliyoyin nairorin da aka riƙa warewa da sunan za a yi wa Majalisa garambawul da kwaskwarima.
“Na farko Channels ta ce an sheƙa ruwan sama. Wannan ba gaskiya ba ce. Na biyu sun ce Zauren Majalisa ya yi yoyon ruwan sama. Wannan ma ba haka ba ne.
“Sai na uku sun ce Majalisa ta amince a yi gyare-gyaren Naira biliyan 37.”
Ya ce ba duka kuɗaɗen aka fara aikin da su naira biliyan 9 ne, saboda kwarona.
Shi kuma Lawan ya yi gargaɗi cewa a guji watsa labarai na ƙad-da-ƙanzon-kirege ba tare da an yi bincike.
“Kuma ni ina da yaƙinin cewa wakilin Channels da ke aiki a majalisa ya na aika masu bayanai, ba shi da hannu a labarin wanda su ka buga saboda da ya san gaskiyar lamarin duk abin da batun kuɗaɗen ke ciki.” Inji Lawan.