Yaya gaskiyar batun cewa Tiwita ya sauya launin inda ake latsawa dan yada labarai zuwa kore dan nuna goyon bayan ta ga zanga-zangar #June12 a Najeriya? Binciken DUBAWA

0

Yayin da ake gudanar da zanga-zangar June 12, ko kuma ranar tunawa da kafuwar dimokiradiyya a Najeriya, wanda ke daukar hankali a shafin Tiwita, wani mai amfani da shafin mai suna @ChibuzorUkwu yana zargin cewa Tiwita ta sauya launin inda ake latsawa dan tura sako. Zargin na cewa a baya, wurin ya kasance ruwan bula/shudi amma an sauya launin zuwa kore dan nuna goyon baya ga Najeriya.

Ra’ayoyin wadanda suka mayar da martanin dangane da wannan batu sun banbanta domin wadansu sun ce dama can launin kore ne a yayinda wasu kuma suka ce nasu har yanzu, launin bai canza ba

Tantancewa

DUBAWA ta gudanar da bincike na mahimman kalmomi wanda ya kai ta ga wani rahoton da jaridar Independent ta wallafa a shekara ta 2016, inda take sanar da cewa twitter ta sauya launin abun latsawa dan tura sakonnin daga launin kore mai duhu zuwa wani launi mafi haske.

Binciken ya kuma kai mu ga wata sanarwar da aka yi a shafin na tiwita a 2016 a shafin Matt Navarra (@MattNavarra) wani dan Birtaniya wanda ke zaman kwararre kan harkokin da suka shafi yanar gizo. Navarra ya yi bayani kamar dai yadda jaridar Independent ta yi.

A Karshe

Babu wani sabon sauyin da aka yi, dama can abun latsawar kore ne. Ko sadda aka sauya launin a 2016, hasken launin kadai a canja da ma kore ne launin kuma dalilin yin hakan ba shi da wata dangantaka da Najeriya. Dan haka wannan labarin ma karya ne.

Share.

game da Author