YAWAN SATAR ƊALIBAI: Gwamnati ta yi amfani da tubabbun mahara su murƙushe gagararrun ‘yan bindiga

0

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci gwamnatin tarayya ta raba kawunan ‘yan bindiga wajen yin amfani da waɗanda su ka ajiye makamai ta yi amfani da su wajen yaƙin kangararrun da su ka ƙi ajiye makamai.

Gumi na magana ne dangane da sace ɗaliban Islamiyya 139 da mahara su ka yi a garin Tegina, cikin Ƙaramar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Jaridar Punch ta ruwaito Gumi na cewa akwai ‘yan bindiga da dama masu so su ajiye makamai, shi ya sa Gumi ya ce idan ire-iren su su ka sasanta da gwamnati, sai ta yi amfani da su ya murƙushe gagararrun da su ka fanɗare.

“Mu dai mu na yin bakin ƙoƙarin mu. Amma su waɗannan ‘yan bindiga sun fi so su yi sulhu da gwamnati. Duk wani sulhu idan babu gwamnati a ciki, to akwai matsala. Kenan dole sai an haɗa hannu biyu kenan, idan ana so sulhu ya yi nasara.”

“Akwai masu so a yj sulhu da su a yaƙi gagararrun da su. Saboda haka gwamnati ta yi amfani da masu ɗan dama-dama ta yaƙi gagararru. Bayan ta kakkabe gagararrun sai kuma ta yi amfani da tubabbun su ta kakkabe masu dama-damar da su ka fanɗare.”

Gumi ya buga misalin yadda fanɗararrun ‘yan Boko Haram (ISWAP) su ka halaka Shekau, bayan Shekau ya shafe shekaru sama da 10 an kasa kama shi ko kashe shi.

“Da yawan su waɗanda mu ka tattauna da su duk su na so su ajiye makamai. To da irin su gwamnati ya kamata gwamnati ta ja a jika ta ba su makamai su yaƙi kangararrun su. Ai babu wanda ba ya son ƙarfi da kuma kuɗi.”

PREMIUM TIMES ta buga labarin da gwamnarin jihar Neja ta ce d
ɗaliban Islamiyya 136 ne aka yi garkuwa da su.

Gwamamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa adadin ɗaliban Iskamiyyar da masu garkuwa su ka sace a garin Tegina na Jihar Neja, su 136 ne.

Mataimakin Gwamnan Neja, Ahmed Ketso ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ƙarin bayani dangane da halin da ake ciki a jihar tun bayan kwashe ɗaliban da aka yi a farkon makon jiya.

Ketso ya tabbatar wa iyayen ɗaliban cewa gwamnati na yin dukkan bakin ƙoƙarin ganin an cefo ɗaliban sun koma gidajen su cikin ƙoshin lafiya.

Ya kuma yi bayanin irin motocin sintirin da gwamnatin jihar ta sai wa jami’an tsaro, har da babura.

An Haramta ‘Yan Acaba A Minna:

Domin ƙarfafa matakan tsaro a jihar, gwamnatin jihar Neja ta haramta haya da baburan achaba a cikin Minna, babban birnin Jihar Neja.

Da ya ke ƙarin bayani, Mataimakin Gwamna, Ahmed Ketso ya ce kada a ƙara ganin baburan ‘okada’ na karakaina a cikin garin Minna.

Haka su ma masu baburan kan su na hawan yau da kullum, an taƙaita zirga-zirgar su, daga ƙarfe 9 na dare zuwa wayewar gari, ƙarfe 6 na safiya.

Haka kuma gwamnati ta umarci dukkan Hakimai da Dagatai da Masu Unguwanni su tabbatar sun riƙa tantancewa, ƙididdigewa da yi wa kowane baƙon da ya sauka cikin al’umma rajistar sanin asali, tare da damƙa bayanan sa a hannun ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron da ke da kusanci da jama’a.

Share.

game da Author