Najeriya kasa ce wacce Allah ya azurtata da matasa, wadanda adadinsu ya kai kusan kaso tamanin na mutanen kasar. Matashi dai kamar yadda majalisar dinkin duniya tace, shine mutumin da yake tsakanin shekara 15 zuwa 35.
Dimokraɗiyya tsarin mulki ne na jama’a, saidai duk mutumin da bai kai shekara 18 ba, bashi da tasiri a cikinta saboda bashi da ‘yancin yin zabe, ballantana tsayawa takara. Bincike ya nuna cewa, babu mulki daidai da Afrika kamar siyasa.
Karanta littafin da John N Paden ya rubuta mai suna Muhammadu Buhari. Saidai zai wahala matasan Najeriya su karbi jagorancin kasar a nan kusa. Ga dalilai:
Abu na farko, talauci yana da tasirin gaske a cikin rayuwarsu. Siyasar Najeriya ta koma babban kasuwanci, wasu sun mayar da ita hanyar samun gwagwgwaɓar riba. Yana da wahala talaka ya iya samun tikiti na takara, ballantana cin zaɓe. Harka ce ta miliyoyin kuɗi, rashin aikin yi ga matasa ya yi yawa. Basu da kuɗin yin takara.
Dalili na biyu shine, rashin kishin kai ga matasa. Masu mulki sun gane cewa matasan Najeriya basu da ra’ayin shiyasa shi ya sa basu shakkarsu a lokacin zaɓe. Babu abinda zasu iya yi saboda an fassarasu a matsayin maroƙa, ƴan jagaliya, kwaɗayayyu da sauransu. Duk mutumin da ya gane kana da kwaɗayi ya gama da kai. Gasu nan tun yanzu sun fara bibiyar wasu mutane masu kuɗi marasa inganci. Kungiyoyi iri-iri na damfara.
Abu na uku shine, buri da mutuwar zuciya. Matasan da suka shiryawa wahala kafin dadi ya zo basu da yawa. To su kuma wadanda suke rike da Najeriya, sun jure wahala kafin su zamo abunda suka zama yanzu. Ku bi tarihin su za ku sha mamaki. Ba su yiwa arziki gaggawa ba. A hankali su ka dinga tafiya har su ka zo matakin da su ka samu kansu yanzu cikin ikon Allah.
Abu na karshe shine, kwaikwayon rayuwar turawa. Wasu daga cikin matasa sun dauko dala ba gammo. Babu soyayyar Najeriya a zuciyarsu. Abun mamaki, suna Najeriya amma tunaninsu na turawa ne. Irin wad’annan matasan babu soyayyar Najeriya a zuciyarsu.
Jin kunya ma su ke yi a kallesu a matsayin ƴan kasar. A wajen irin wad’annan matasan za a samu “nationalism”? Irin wannan ƙalubalen ne su Walter Rodney suka dinga fada da shi. Matsalar Najeriya daban da ta turawa.
Allah ya shiryar da mu.