‘Yan Siyasa Da Al’ummar Jihar Zamfara, Don Allah Ku Taru Ku Goyawa Gwamna Matawalle Baya, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Ya ku Jama’ah, kamar yadda kuka sani ne, ana nan ana ta cece-kuce da surutai, game da maganar barin Gwamna Matawalle tsohuwar jam’iyyar sa, tare da komawa wata jam’iyyah. Kowa yana ta kokarin fadin albarkacin bakin sa akan wannan al’amari. Wasu suna ganin dacewar yin hakan, wasu kuma suna ganin rashin dacewar yin hakan.

To koma dai menene, mu fatan mu da addu’ar mu shine, rokon Allah ya bashi ikon sauke nauyin da Allah ya dora masa, na hakkin kula da ilahirin Zamfarawa. Kuma ina addu’a da rokon Allah, yasa komawar Gwamna Matawalle wata jam’iyyar, ya zamar wa jihar Zamfara da Zamfarawa alkhairi. Allah ya bashi iko da basirar gano bakin zaren matsalar rashin tsaro da ta dabaibaye jihar mu ta Zamfara, amin.

Game da ‘yan uwana, ‘yan siyasar jihar Zamfara kuwa, manyan su da kananan su, da ‘yan uwana ilahirin Zamfarawa, ina rokon ku, domin Allah, domin kaunar da kuke yiwa Manzon Allah (SAW), ku ajiye duk wata maganar adawar siyasa, da wasu bambance-bambance, ku hada karfi da karfe, ku tallafawa Gwamna Matawalle, domin samun nasarar tunkarar matsalolin jihar mu mai albarka!

Ku sani, ya ku ‘yan siyasa da jama’ar jihar Zamfara, wallahi halin da jihar mu take ciki a halin yanzu, ba ya bukatar a samu wata maganar adawa ko kuma magana akan wata jam’iyyar siyasa. Abu ne da kuka sani a fili karara cewa, muna cikin mummunan hali na rashin tsaro, wanda ya hana jihar mu ci gaba. Saboda haka domin girman Allah, ina kiran da ku ji tsoron Allah, ku sani, dukkanin mu, zamu mutu, mu tsaya gaban Allah, domin amsa tambayoyi, akan duk abunda muka aikata a wannan rayuwar tamu ta duniya!

Ku sani, Gwamna Matawalle yana bukatar addu’o’in ku da goyon bayan ku matuka. Idan kuwa bai samu wannan ba daga gare ku, to babu yadda za’a yi yaci nasarar ciyar da jihar Zamfara gaba. Don haka don Allah kuyi hakuri, ku goya masa baya.

Ina kira ga duk wani dan siyasa a jihar Zamfara, da dukkanin Zamfarawa, da muji tsoron Allah, mu taru, kwan-mu-da-kwarkwatar mu, mu taimakawa wannan bawan Allah, domin jihar mu ta samu zaman lafiya da ci gaban da ya kamata.

Game da tsohon Gwamna, wato Alhaji Abdul’azizi Yari, shi da magoya bayan sa duka, don Allah ina kira da rokon ku, ku manta da duk wata adawar siyasa, ku manta da duk wani abu da ya faru a can baya, ganin irin halin da jihar mu take ciki! Ku goyi bayan gwamnatin Matawalle, domin samun zaman lafiya da ci gaba mai dorewa!

Sannan ina rokon Jagoran siyasar jihar Zamfara, Mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, kuma tsohon Sanata, kuma dan takarar shugabancin Najeriya, wato Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, da manyan ‘yan siyasar jihar Zamfara, irin su, Alhaji Dauda Lawan Dare, da Alhaji Aminu Sani Jaji, da Sanata Kabiru Marafa, da Malam Wakkala, da Alhaji Abu Magaji, da Alhaji Sagir Hamidu, da Alhaji Mansur Dan Ali, da Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, da Sanata Sa’idu Dansadau, da Wamban Shinkafi, da Alhaji Bashir Yuguda, da Alhaji Ibrahim Shehu Bakauye, da dukkanin Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai na jiha da na tarayya, da ministocin da suka fito daga jihar Zamfara, da kwamishinoni, da shugabannin kananan hukumomin jihar Zamfara da kansiloli; Sarakunan jihar Zamfara, da Malaman addini, da ‘yan Bokon jihar Zamfara, kai da dukkanin wasu manyan ‘yan siyasa da kanana na jihar Zamfara, da ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara, da ‘yan kasuwar jihar Zamfara, da dukkanin Zamfarawa, da domin Allah su hada kai, su zama tsintsiya madaurinki daya, su goyi bayan Gwamna Matawalle, domin dawo da tsaro da ci gaba, da dawo da martabar jihar mu.

Ku sani, wallahi, idan kuka ki yin haka, dukkanin ku zaku mutu, kuma zaku tashi gaban Allah Subhanahu wa Ta’ala, domin ku amsa tambayoyi, akan kin bayar da gudummawa da goyon baya da hadin kai, domin ci gaban al’ummar ku, akan damar da ya baku, ta zama jagororin siyasa a jihar ku.

Don Allah ina rokon ku, ku manta da duk abunda ya faru tsakanin ku a can baya, yanzu kuyi kokari, ku ceci al’ummar ku daga ci gaba da rugujewa. Kuna sane, jihar Zamfara da Zamfarawa suna cikin wani irin mummunan hali marar dadi na barayi da ‘yan ta’adda da suke addabar al’ummah. Wadannan ‘yan ta’adda sun jawo rushewar kasuwanci da rushewar harkar noma da kiwo, da sauran harkokin yauda-kullun na jihar Zamfara.

A can baya, duk inda mutum ya shiga a nan gida Najeriya, kai wallahi da ma duniya baki daya, da zaran mutum yace shi dan jihar Zamfara ne, wallahi zaka ga ana son sa, ana kaunar sa, ana ribibin sa; kowa yana son ganin sa, albarkacin maganar Shari’ar Musulunci da Sanata Ahmad Sani Yariman ya kawo. Amma yanzu halin ta’addacin nan da ‘yan ta’adda da ya bata sunan jihar, da zarar kace kai dan jihar Zamfara ne, to wallahi kallon da za’a yi maka shine, mutumin da ya fito daga jihar barayi, ‘yan ta’adda (armed bandits).

Saboda haka, hakki ne da ya wajaba ga duk wani Bazamfare, a duk inda yake, ‘yan siyasa da magoya bayan su, su bayar da gudummawa, wurin kawo karshen wannan ibtila’i.

Daga karshe, ina rokon Allah ya baku ikon hada kai, da taimakawa Gwamna Matawalle a jagorancin sa, domin samun nasarar gyaran lamurran jihar Zamfara, amin.

Wassalamu Alaikum

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuta. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author