‘Yan sanda sun kama wani shirgegen mutum da ya yi wa ‘yar shekara 9 fyade

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta kama Kelvin Abugu mai shekara 35 da laifin yi wa ‘yar shekara 9 fyade.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bolaji Salamiya sanar da haka a Akure ranar Laraba.

Salamiya ya ce mahaifiyar yarinyar ce ta kawo kara ofishin’ yan sandan.

“Mahaifiyar yarinyar ta ce ta ga ‘yarta na fitsari da jini ne, daga nan sai hankalinta ya tashi, sai ta tambaye ta lafiya kuwa take fitsari da jini, bude bakin yarinya kuwa sai ta ce wani ne mai suna Abugu ya yi lalata da ita da karfin tsiya.

Salamiya ya ce bayan haka ne jami’an tsaro suka je suka kamo Abugu inda bayan an tunhumesa ya bayyana cewa lallai da gaske ya aikata haka.

Ya ce rundunar ta kammala bincike sannan za ta Kai Abugu kotu da zaran kotu ta janye yajin aikinta.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda jami’an tsaro na Sibul Difens, NSCDC, reshen dake jihar Anambra ta kama wani magidanci mai shekaru 48 mai suna Thomas Igbo da aka samu da yin lalata da ya’yansa mata uku.

Igabo ya rika lalata da ‘ya’yan sa wanda suke da shekaru 8, 3 da 1 da rabi.

Da ‘yan sanda Suka kama shi Igabo ya ce ya kan kwana da babbar ‘yarsa mai shekara 8 da karfin tsiya, su kuma sauran masu shekara 3 da daya da rabi ya na saka musu yatsu a gaban su ne.

Share.

game da Author