A ranar Laraba kotun majistare dake Gwagwalada Abuja ta gurfanar da wasu mata biyu da suka kware wajen satar.
‘Yan matan masu suna Magdalene Innocent mai shekara 22 da Godiya Zingdam mai shekara 22 mazaunan kauyen Nuwamlenga hanyar zuwa tashar jiragen sama da ke Abuja.
Magdalene da Godiya sun saci gwala-gwalan da ya kai naira 740,000, talabijin, atanfuna, leshi da tsaban kudi har naira 318,000 a gidan wani makwabcin su.
Makwabcin mai suna Muhammed Isah da ya ga aika-aikan da aka aikata sai ya kai kara ofishin ‘yan sanda ranar 31 ga Mayu.
A kotun Magdalene da Godiya sun musanta aikata haka.
Daga nan lauyan dake kare Magdalene da Godiya, Leslie Mukoro ta roki alkalin da ya bada belin sun su bisa ga tsarin dokan hukunta barayi.
Alkalin kotun Aliyu Shafa ya bada belin matan sannan ya ce kowace za ta biya kudin belin naira 500,000.
Sauran sharuddan belin sun hada da gabatar da shaidu biyu dake da katin zama dan kasa kuma suna zama a wurin da kotu take.
Za a ci gaba da Shari’a ranar 26 ga Yuli.
Discussion about this post