‘Yan sanda sun cafke magidancin da ya yi lalata da ‘yarsa da kuma hadiman sa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta damke wani magidanci mai suna Kingsley Achugbu mai shekaru 35 da ya yi wa ‘yarsa mai shekara biyu da mai aikinsa fyade.

Kakakin rundunar Muyiwa Adejobi ya sanar da haka ranar Talata.

Adejobi ya ce ‘yan sandan sun kama Kingsley ranar Litini a gidansa dake Festac bayan mai aikin ta kawo kara ofishin ‘yan sanda.

“Jin haka ya sa muka gaggauta muka kamo Kingsley ranar 21 ga Yuni.

Ya ce likitoci na duba karamar yarinyar tare da mai aikin.

Bayan haka kwamishinan ‘yan sandan jihar Hakeem Odumosu ya ce rundunar a shirye take domin ta yaki matsalolin cin zarafin mata da yara kanana a jihar Kai tsaye.

Odumosu ya ce yaki da cin zarafin mata da yara ya zama dole ganin yadda matsalar ya zama ruwan dare a jihar da kasa baki daya.

Idan ba a manta ba a ranar Talata ne kotun majistare dake ikeja jihar Legas ta yanke wa Gabriel Audu hukuncin zama a kurkuku har sai ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifi na jihar.

Alkalin kotun A.O. Layinka ya yi watsi da rokon sassauci da Audu ya yi sannan ya ce za a ci gaba da Shari’a ranar 6 ga Yuli.

Audu mai shekaru 25 mazaunin Ikeja ne kuma kotun ta kama shi da laifin yi wa ‘yar shekara bakwai fyade da yi mata barazanar zai kashe ta.

Share.

game da Author