‘Yan Najeriya sun yaba wa Buhari nadin tsoffin hafsoshin Najeriya jakadun Kasashen Afirika dake da mahimmanci ga tsaron Najeriya

0

Idan ba a manta ba tun bayan yin murabus da manyan hafsoshin tsaron Najeriya suka yi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada su jakadan Najeriya, sai dai bai ayyana ko wacce kasa ce za su yi aiki ba.

A ranar Laraba, Shugaban ya fadi Kasashen da zasu yi aiki.

• Lt Gen. Tukur Buratai (Rtd) = Benin Republic

• Air Marshal Saddique Abubakar (Rtd) = Chad

• General Abayomi Olonisakin (Rtd) = Cameroon

• Air Vice Marshal Sani Usman (Rtd) = Niger

• Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas (Rtd) = Ghana

‘Yan Najeriya sun yaba wa shugaba Buhari kan wannan nadi da yayi na manyan hafsoshi, inda ya tura kasashen da suka fi muhimmanci ga Najeriya musamman game da tsaro.

Share.

game da Author