Ƴan bindiga a Jihar Katsina sun bindige Mohammed Ahmed, Ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Zamfara, jim kaɗan bayan ya halarci bikin canjin sheƙar su da Gwamna Matawalle daga APC zuwa PDP, a ranar Talata.
Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Matawalle, Yusuf Idris, ya ce an bindige shi ne ranar Talata a tsakanin ‘Yankara da Sheme, cikin Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Honorabul Ahmed na kan hanyar sa ne ta zuwa Kano domin ya raka wani ɗan sa ya hau jirgin sama zuwa Sudan, inda ya ke karatu a can, sai ba kai ga isa ba, ƴan bindiga suka harbe shi.
Yusuf Idris ya ce Ahmed shi ne Shugaban Kwamitin Lura da Kasafin Kuɗi na Majalisar Tarayya kafin rasuwar sa.
An rufe shi a safiyar Laraba a Gusau, bayan an yi masa Sallar Janaza a Masallacin Sheikh Umar Kanoma da ke kan hanyar Sokoto by-pass a Gusau.
Cikin waɗanda su ka halarci jana’izar sa, har da Gwamna da tsoffin Gwamnonin Zamfara, Ahmed Yarima da Mamuda Shinkafi da tsoffin Mataimakan Gwamna biyu.
Discussion about this post