Yadda yunwa ta sa tilas na rungumi harkar noma – Mace mai digiri na biyu

0

Wata mata wadda ta yi Digiri na Biyu, wato Masters Degree kan Tsarin Kasuwanci, ta bayyana wa PREMIUM TIMES yadda yunwa ta sa ta kama harkar noma ka’in-da-na’in.

Dunmola Sodeke ita ce Shugabar Gonar Omodun Farms, kuma a Jami’ar Aberdeen ta kasar Scotland ta yi Digiri na Biyu.

Mijin ta ya mutu ya bar ta da ‘ya’ya biyu. Amma har ta mallaki gonaki a Jihohin Lagos, Kwara, Abeokuta da Ibadan.

Ta na noma kayan miya kamar ganyen alayyahu da sauran su. Sannan ta na noma waken soya, masara, kuma ta na da babban kandamin da ta ke kiwon kifaye masu yawan gaske.

Ta shaida wa wakilin mu cewa a yanzu haka akwai ma’aikata a karkashin ta masu kula sa gonakin ta, su 25.

“A baya kafin na fara noma, ina aiki a kamfanin Exxon Mobil. Sai wani dan sabani ya shiga, dama ni ba ma’ikaciyar dindindin ba ce. Da wa’adin aiki na ya kare, sai na fara zaman-kashe-wando.

“Sannan kuma miji na ya mutu cikin 2015. To bayan na rasa aikin yi, ga miji na ya mutu, sai na fara tunanin ta yaya zan iya kuma zan rika ciyar da yara biyu da ya mutu ya bari?

“To dama ina sha’awar noma, kuma mahaifi na ya na da gonaki da yawa. Sai na fara tunanin shin na yi noma ne ko kuma na bude ‘Suoer Market’?

“Na je na fara aiki a wata Super Market, wai don na nakalci yadda sana’ar ta ke kafin na bude tawa. Amma sai na gane lallai ba ni da rabo a Super Market, domin abin ba yadda na dauke shi ya ke ba.

“Ina nan sai wani kawu na ya ba ni shawarar shiga harkar noma kawai.”

Ta ce daga nan sai fara sha’awar kiwon kaji, bayan ta yi kwas na watanni uku a Songhai. Kuma ta fara har da noman kayan miya da kiwon kifaye.

“A gaskiya dai zan iya ce maka ni tsoron kada yunwa ta danne ni da yara na ya sa na kama sana’ar noma gadan-gadan.”

“Na sha wahala kafin na samu gonaki. Mata na samun matsalar samun sayen gonaki ko karbar gonaki jingina ko aro. Sai da na hada da wasu ‘yan-kore sannan na samu gonakin. Yanzu aka akwai gonar da na karba aro a yarjejeniyar tsawon shekaru biyar.

Ko ta fara fitar da kayan gonar ta kasashen waje? Sai ta ce ba ta fara ba rukunna, saboda akwai masu saye a nan gida, ba ta da matsalar kwastomomi.

Sai dai ta ce ta kan sayi irin da ta ke shukawa ne a Kalaba da Ekiti, sannan kuma ba ta amfani da takin zamani, domin irin noman ta ba mai bukatar takin zamani ba ne.

Sai dai kuma ta yi kukan cewa komai ya kara tsula tsadar tsiya a yanzu.

“Irin shukar da mu ke saye naira Naira 350 a ‘yan shekarun baya, a yanzu naira 30,000 ake sayarda shi). Inji ta.

“Na taba noma gurjin kwakwamba a wata gona na samu cinikin naira miliyan biyu. Wadannan kudin na dauka na sayi wata gonar kuma.”

Ta ce ba ta taba cin moriyar tallafin gwamnati ba. “Saura kadan talalfin Shirin FADAMA ya zo hannu na, amma sai rabon bai zo kai na ba.” Cewar ta.

Share.

game da Author