Yadda ‘yan uwan mijina suka tilasta ni na sha ruwar da aka wanke gawar mijina – Matar mamaci

0

A ranar Lahadi wata mata Chioma Asomugha mai shekaru 34 a karamar hukumar Ubahuekwem jihar Anambra ta kai kukanta ofishin hukumar NHRC bayan ‘yan uwan mijinta sun tilasta ta sha ruwar da aka wanke gawar mijinta.

Chioma ta ce kafin mijinta Charles ya rasu suna zama ne a Ajangbadi dake Ojo kiss a jihar Legas kuma suna da ‘ya’ya hudu tare.

Ta ce bayan mijin ta ya rasu sai suka dawo gida domin yin jana’izar sa da yin zamammakoki. ‘Yan uwan mijin suka koreta daga gidan sun sannan suka bata ruwar da aka wanke gawar mijin nata ta sha wai domin a tabbatar cewa ba itace ta kashe dan uwan su ba.

“Ganin haka ya sa na ruga ofishin kare ‘yancin dan adam, NHRC domin su kwato min hakki na kuma kai kara wajen manyan dake kauyen domin su hana ‘yan uwan mijina tozarta ni.

“A halin da nake ciki yanzu ‘yan uwan mijina sun hakikance ba fa zan zauna a gidan da mijina ya rasu ya bari ba kuma suka hani halartar jana’izar sa wanda aka yi ranar litinin.

Daya daga cikin dattawan kauyen Ubahuekwem Gerald Nnabugwu ya bayyana cewa dattawan kauyen za su dauki mataki domin kawo karshen matsalar.

Sannan shima kwamishinan yada labarai C-Don Adinuba ya ce gwamnati za ta sa baki domin kwato was Chioma hakkin ta.

Share.

game da Author