Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa tadamke wani matashi mai suna Ibrahim Haruna mai shekaru 25 da ya yi wa ‘yar shekara 6 fyade.
Mataimakin kakakin rundunar Lawan Adam ya sanar da haka ranar Talata a garin Hadejia.
Adam ya ce Haruna mazaunin kwatas din Gawuna ne dake karamar hukumar Hadejia sannan yana da shagon siyar da kayan masarufi a garin.
Adam ya ce wata rana Haruna ya lallabi yarinyar zuwa shagon sa inda a nan ne ya yi lalata da ita da karfin tsiya.
Ya ce rundunar ta samu labarin haka ranar 17 ga Yuni bayan mahaifiyar yarinyar Maryam Kani ta kawo kara a ofishinsu.
Adam ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifi irin haka zai ci gaba da gudanar da bincike akai.
A watan Mayu rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa ta saurari kararrakin fyade 35 a cikin watanni hudu a jihar.
Bisa ga kararrakin da ta saurara rundunar ta ce ta saurari kararrakin fyade fiye da sauran laifuffuka kamar su garkuwa da mutane da kai wa mutane hari.
Yi wa yara kanana fyade ya zama ruwan dare a kasar nan.
Abin tambaya a nan shine wai da wani manufa ne masu yi wa yara kanana fyade suka tunkarar su da shi.
Shin abin tsafi ne, rashin tarbiya ne ko kuma rashin tsoran Allah?