Yadda wata Uwa ta siyar da ya’yanta biyu naira N300,000 saboda tsananin talauci

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wata mata mai suna Blessing Ebuneku mai shekaru 35 da ta siyar da ‘ya’yan ta mata biyu akan Naira 300,000.

Blessing ta siyar da Semilore Agoro mai shekara 4 da Deborah Agoro mai shekara 2 akan naira N150,000 kowannen su.

Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar da haka ranar Lahadi yana mai cewa rundunar ta kama matar ne bayan mijinta kuma mahaifan ‘ya’yan ya kawo kara a ofishin ‘yan sanda.

Oyeyemi ya ce Blessing wacce ke tsare a ofishinsu ta bayyana cewa ta siyar da ‘ya’yanta saboda rashin kudin kulawa da su.

“Agoro ya bar gida shekaru biyu da suka wuce sannan tun da ya tafi yadda kasan an aiki bawa garinsu ba mu sake ji daga gare shi ballantana sakon kudin abinci.

“Sannan ni gashi bayan da mijina ya tafi na yi alaka da wani masoyina har na haihu masa shima ‘ya’ya biyu. Kula da ‘ya’ya hudu ya zama da wahala.

“Yayin da nake fama da fatara ta ne na hadu da wani Kolawole Imoleayo inda ya hada ni da wasu mutane mata da miji dake zama a fatakwal Kuma suna neman ‘ya’ya inda na siyar musu da ‘ya’yana mata biyu akan Naira 300,000.

Oyeyemi ya ce mahaifin ‘ya’yan Agoro ya ce bayan ya dawo gida daga tafiyar da ya yi ne ya ga babu ‘ya’yan sa mata biyu a gidan. Ko da ya tambayi matar sa sai taki gaya masa inda suke.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edward Ajogun ya bada umurin a kai file din laifin da Blessing ta aikiata zuwa fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka domin ci gaba da gudanar da bincike da ceto yaran da aka siyar.

Share.

game da Author