Yadda wani mafusaci ya gaura wa shugaban kasar Faransa mari sai da ya kife, daga mika masa hannu su yi masabaha

0

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sha zazzafar mari daga wani mutum da ba a faɗi sunan sa ba a lokacin da shugaban kasar yayi kokarin kai masa hannu su yi masabaha.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan yanar gizo, musamman Soshiyal Midiya, an ga shugaba Macron na Faransa sanye da rigar sa fara kamar yadda ya saba sannan kuma da takunkumin fuska ya garzaya wajen wasu gungun masu zanga-zanga a can gefe.

Isar sa ke da wuya sai ya mika wa wani da ke tsaye cikin gungun masu zanga-zanga hannu su gai sa, shi ko gogan naka daga mika masa hannu sai ya ɗaga hannun sa ya gaura wa shugaban Macron mari sai da ya fike.

Daga nan sai jami’an tsaro suka diran mmasa, suka kubutar da shugaban kasa Macron sannan suka waske da shi cikin mota aka yi gaba da shi.

Shi kuma wanda ya aikata abin da wani abokinsa a kife na fuskantar tambayoyi daga jami’an tsaron kasar.

Wannan ba shine karo na farko da ake yi wa shugaban kasar irin haka ba , an taba yi masa a lokacin yana minista a 2016. Sai dai wannan lokaci ba marin sa aka yi ba, wani ne ya jefasa da ɗanyen kwai a wajen taro.

Share.

game da Author