Yadda gara ta cinye sakandare sukutum bayan an karkatar da naira miliyan 30 ta maganin ƙwari

0

A wani abu mai ban-al’ajabi da ya faru jihar Ekiti, gara da zago sun kori ɗaliban makarantar sakandare ta Osi Community High School, da ke Osi Ekiti a cikin jihar.

Gara da zago ne su ka mamaye ilahirin makarantar cikin ajujuwa da waje, ya yadda tilas aka gudu daga makarantar.

Tun farko dai an kafa wani bincike da wakilin mu ya yi, wanda ya fallasa cewa gwamnati ba ta yi komai na magance gara da zagon ba, waɗanda tuni sun lalata gine-gine, ajujuwa, tebura, kujeru da rufin ajujuwa.

Gara da zago sun kuma gurgure sili da ƙofofi da tagogi baki ɗaya. Da yawan wasu abubuwan ma har saman rufin su duk sun rufto ƙasa.

Inda matsalar ta ke shi ne yadda aka yi sakaci gara da zago su ka lalata makarantar baki ɗaya, bayan an cire kuɗi har naira miliyan 30 wanda za a yi wa ƙwarin feshin magani.

Sannan kuma bincike ya nuna babu ya kuɗin sama da ƙasa babu, kuma ba a kashe ko da gara da zago ɗaya ba.

Kwamiti ya nuna cewa ginin ya lalace, wanda saboda rashin magance zagon da aka yi da waɗannan kuɗaɗen tun da farko, a yanzu sai an kashe maƙudan kuɗade kafin a gyara makarantar.

Yayin da wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya isa ƙofar makarantar, ya ga irin mummunar ɓarnar da zago da gara su ka yi a wajen haraba da cikin filin makarantar da kuma cikin ajujuwa.

Zago da gara sun cinye kusan dukkan itatuwan da ke wajen makarantar. Sannan kuma duk inda ka duba hagu da dama duk tulin shurin ƙasa ne wanda gara da zago su ka yi.

Babu wani abu da waɗannan ƙwari ba su lalata ba.

Wani malamin ‘Biology mai suna Lawrence Ogunleye ya shaida wa wakilin mu cewa tilas ta sa aka kwashe ɗalibai daga makarantar, saboda ɓarnar da zago da gara su ka yi, ta yi matuƙar muni.”

Shugaban Makarantar Abiodun Aladelesi ya shaida wa wakilin mu cewa sun yi iyakar ƙoƙarin su, amma abin ya fi ƙarfin su.

“Akwai lokacin da mu ka yi feshin magani, amma hakan bai hana zago da gaza ci gaba da yi mana ɓarna ba.” Inji shi.

Cikin 2017 dai Gwamnatin Jihar Ekiti ta ware naira miliyan 30 domin a magance ƙwarin, amma ko guda ɗaya ba a kashe ba, kuma an kashe kuɗaɗen.

Share.

game da Author