Yadda Fyade ya yi Tsanani a Jihohin Arewa: Shin Talauci ne, Tsafi ne, Tarbiyya ce ko sakacin Iyaye?

0

Wani abu da ya zama ruwan dare a kasar nan yanzu kuma yake ta da wa iyaye hankali shine yadda yi wa yara kanana masu shekara ƙasa da biyar ko sama kadan fyade.

A duk lokacin da ka shiga shafukan jaridu ko shafukan soshiyal midiya a yanar gizo ko kuma a wajen sauraren radiyo ko kallon Talbijin ba zai yi wuya a kammala labarai ko karatu ba, ba ki ji an karanto labarin wani yayi wa karamar yarinyar da ya isa ya haifa ko kuma ma ya yi jika da ita fyade ba.

Sannan kuma abinda zai bakanta maka rai shine duk da akwai dokoki da aka saka domin hukunta irin wadannan mutane da dama daga cikin su kan kubuta ba a hukunta su ba.

Su kuma wadanda a ka zalinta ko oho.

Wasu da dama shikenan an bata musu ‘ya’ya kenan, wasu kuma ko sun girma abin zai cigaba da bijiro musu a duk lokacin da suka tuna sai sun ji ba dadi.

Abin tambaya a nan shine wai da wani manufa ne masu yi wa yara kanana fyade suka tunkarar su da shi.

Na farko dai idan dadi ne namiji ke son ya samu, wannan ‘yar yarinya bata kai ta wadatar da shi ba, saboda haka lallai akwai abinda ya wuce haka.

Da yawa daga cikin wadanda suke aikata wannan abu, akan alakanta su da ko matsafa ko kuma jaraba.

Shin abin tsafi ne, rashin tarbiya ne ko kuma rashin tsoran Allah?

Baya ga maida hankali da iyaye ya kamata su rika yi, ita ma gwamnati sai ta tsananta hukunci akan wadanda aka kama suna aikata wannan abu.

Wasu manazarta sun zakulo wasu hanyoyi da suke ganin za su yi tasiri matuka wajen rage aukuwar yawa-yawan fyade da ake yi wa yara kanana har da manya.

1. A hana ko a rage yawan aikawa da yara hutu gidajen ‘yan uwa, kakanni da abokan arziki ba tare da an tanadi kyakkyawar hanya da za a rika kula da saka musu ido ba. Domin bincike ya nuna makusantar yaran ne suka fi aikata haka akan yaran harda manya ma.

Mafiyawan lokuta ‘yan uwan iyayen yaran Wanda aka fi amincewa da su ne ke aikata irin wannan abu alokacin da suka faki babu wani babba a kusa da su.

Idan ya kama dole a je hutu uwa ta tabbatar ta tafi hutun tare da ‘ya’yan ta domin ta rika saka musu Ido a koda yaushe sannan tana kula da zirga-zirgar su.

2. A daina daukan mai raino, yarinyar zama da masu aiki ba tare da an tantance su sannan ana sa musu ido, ana bibiyar mu’amularsu da yaran gida.

Idan mace baza ta iya yin aikin cikin gidanta ba za ta iya daukar hadima na jeka-ka-dawo, wanda za ta zo ta yi aiki ta tafi.

3. Tarbiya

Rashin baiwa ‘ya’ya tarbiyya na gari na daga cikin abubuwan da ke bata su tun suna kanana. Sai kaga iyaye sun bar yaro tun yana karami yana kalle-kallen da bai kamata ba, wasu iyayen hatta fina-finan batsa suke kallo tare da ‘ya’yan su, wasu ma har saduwa da juna sukan yi a daki daya da ‘ya’yan su.

Sannan kuma da ba yaro tun yana karami damar yin abinda ya ga dama, a barshi kullum a jikin wannan namijin, wai kawon sa ne, wancan namijin wai baffan sa ne.

4 – Sa yaro a hanyar sanin Allah da tsoron sa da kuma nuna masa cewa ga irin abubuwan da zai rika yi idan baki suka zo ko kuma suka je unguwa. Kuma da zaran bai gamsu ba da wani abu da wani ya yi masa ya gayawa iyayen sa.

Share.

game da Author