Yadda daliba ta rasu a dakin kwannan ɗalibai a BUK – Mahukunta

0

Jami’in dake kula da harkokin ɗalibai, na jami’ar Bayero da ke Kano Shamsuddeen Umar ya bayyana cewa wata daliba mai suna Mercy Sunday ta rasu a ɗakin kwanan ɗalibai na Ramat Hall dake jami’ar ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito haka bayan tabbatar mata da aukuwar abin da Shamsuddeen Umar ya yi.

Umar ya ce kwanaki biyu kafin ta rasu ta fara rashin lafiya, amma kuma ta samu kyakkyawar kula a asibitin dake jami’ar, bayan an dubata aka bata magani ta koma daki.

A wannan lokaci har ta samu sauki.

Wata ƙawarta ta ce Mercy ta rasu da safiyar Talata kwance a ɗakinta bayannjikin ya tashi ranar Litini kuma har an sake duba ta.

Marigayiya Mercy na karatu a ɓangaren Kimiyyar Siyasa, a jami’ar ta Bayero.

Share.

game da Author