Yadda Benson, Iraboh da Markus su ka damfari Sakkwatawa naira biliyan 3.5-EFCC

0

Reshen Hukumar EFCC da ke shiyyar Sokoto ya samu gagarimar nasarar camƙe riƙaƙƙun ‘yan damfara, waɗanda su ka damfari Sakkwatawa har naira biliyan 3.5 da sunan su zuba jari a yi hada-hadar ‘ƙwandala cinikin mai kasada’, wato cyrptocurrency da kuɗaɗen su.

Shugaban EFCC na Shiyyar Sokoto, Bawa Kaltungo, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan damfarar sun damfare maƙudan kuɗaɗen jama’a a bankunan UBA, Zenith da GTB.

Bincike ya gano cewa mutum uku da aka kama, Benson Kufre John da Iraboh Eceosa da wani mai suna Markus, sun sayi kantama kantaman gidaje da tantsama-tantsaman motoci na gani na faɗa a Lagos, Fatakwal da Calabar.

Kuma duk EFCC ta samu nasarar ƙwace kadarorin na su da ma wasu kadarorin daban.

Bawa ya shaida wa manema labarai cewa an kwashe watanni tara ana bincike, inda aka gano Sunday Markus ne su ka yi amfani da shi su ka yi wa kamfanin gare rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Kasa (CAC).

EFCC ta gano cewa Markus ya yi amfani da lambar adireshi na bogi. Haka kuma dukkan lambobin wayoyin da ya bayar a matsayin lambar tuntuɓar kamfani, duk ba a yi masu rajista ba.

Mutanen da ke cikin harƙallar sun fi uku. EFCC ta ce sauran sun sulale, amma ana farautar su.

Share.

game da Author