Yadda ƴan bindiga su ka buɗe wa motocin tawagar Ganduje wuta, su ka raunata ƴan sanda uku

0

‘Yan bindiga sun yi wa ayarin motocin rakiyar Gwamna Abdullahi Ganduje ruwan wuta, har su ka ji wa ‘yan sanda uku rauni.

Tawagar dai ta faɗa tarkon ‘yan bindigar a daidai kan iyakar Zamfara da Katsina a ranar Laraba ɗin nan a lokacin da su ke kan hanyar komawa Kano daga Zamfara, wajen bukin canjin sheƙar Gwamna Matawalle, daga PDP zuwa APC.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Muhammad Garba, ya shaida wa BBC cewa, lamarin bai ritsa da Gwamna Ganduje ba, domin ya rigaya ya wuce a cikin ayarin Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa, a lokacin da aka buɗe wutar.

Sai dai ya ce mahara sun buɗe wuta kan motoci biyu da ke cikin ayarin.

“Sun harbi motar Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) da kuma motar ɗaukar marasa lafiya (Ambulance).

“Sun kuma ji wa ‘yan sanda uku rauni, waɗanda ke cikin jami’an tsaron da su ka yi musayar wuta da su. An kai su asibiti, an duba lafiyar su, har an sallame su.”

An kai wannan hari kwana ɗaya bayan ‘yan bindiga sun bindige Ɗan Majalisar Tarayya na Zamfara, ranar da su ka canja sheƙa zuwa APC.

‘Yan bindiga a Jihar Katsina sun bindige Mohsmmed Ahmed, Ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Zamfara, jim kaɗan bayan ya halarci bikin canjin sheƙar su da Gwamna Matawalle daga APC zuwa PDP, a ranar Talata.

Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Matawalle, Yusuf Idris, ya ce an bindige shi ne ranar Talata a tsakanin ‘Yankara da Sheme, cikin Ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Honorabul Ahmed na kan hanyar sa ne ta zuwa Kano domin ya raka wani ɗan sa ya hau jirgin sama zuwa Sudan, inda ya ke karatu a can.

Yusuf Idris ya ce Ahmed shi ne Shugaban Kwamitin Lura da Kasafin Kuɗi na Majalisar Tarayya kafin rasuwar sa.

Share.

game da Author