Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa ya yi horo da a rika yi wa duk wanda zai shiga siyasa musamman wanda zai yi takarar wata kujera ta siyasa al gwajin ƙwaƙwalwa, ko ya na ta’ammali da muggan kwayoyi.
Buba Marwa ya faɗi haka a hira da yayi da BBC Hausa ranar Juma’a.
Marwa ya ce cikin kowani ɗan Najeriya 7 akwai mutum daya dake ta’ammali da kwayoyi masu jirkita ƙwaƙwalwa.
” Ni a nawa ganin idan har za a yarda cewa sai dole an yi gwajin cutar HIV, da na sanin kwayoyin halittar mutum wato ‘Genotype’ kafin a yi aure, ya kamata a tilasta yin gwajin ta’ammali da kwayoyi, a sani ko angon ko amaryar ƴan maskewa ne, kar sai anyi kuma abu ya yamutse.
” Zuwa yanzu hukumar mu ta kama muggan kwayoyi masu nauyin sama da kilo giram miliyan 2, sannan mun kama masu safara da siyarwa har sama da mutum 2000.
” Sannan kuma muna ba iyaye shawara da su rika saka wa ƴaƴan su ido matuka. A rika sanin yara suke zuwa, da wa suke fita, da su wa suke yawo, yaya yanayin jikin yaro, idanuwan su sukan kaɗa a wasu lokuttan ko kuma ma kalaman su kan canja, yadda ba haka ya saba a baya ba. Dole sai an sa ido sosai.
Marwa ya ce idan ba haka iyaye ke yi ba, toh ko wata ran za su wayi gari ne kawai su ga yaro ya daɗe da afkawa cikin harkar shaye-shaye da sauran su.
” Jihar Kano ta fara yin irin wannan gwaji. Kuma ina yaba wa gwamnan jihar Ganduje. Duk wanda zai naɗa kowane muƙami sai an yi masa gwajin kwaya.
Discussion about this post