TSUNTSU DAGA SAMA GASASSHE: Canada ta ba Najeriya dala miliyan 27 tallafi ga ƴankunan da Boko Haram su ka kassara

0

Gwamnatin Canada ta bada sanarwar ware dala har miliyan 25.95 domin bayarwa ga Najeriya matsayin gudummawar agaji, domin samar da kayan abinci da abinci mai gina jiki, ruwa, kayan tsaftar jiki da muhalli da kuma ayyukan samar da tsaro a yankunan al’ummar da Boko Haram su ka tauye wa rayuwa.

Ofishin Jakadancin Kasar Canada a Najeriya da ke Abuja ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce za ta bayar da kuɗaɗen ne domin inganta rayuwar al’ummar yankin Arewa maso Gabas da Boko Haram ya haifar masu koma-baya a dukkan fannoni na ci gaba da inganta rayuwa.

“Wannan ƙazamin tashin hankali da ya shafe fiye da shekaru goma ana fama, ya haifar da ɗaya daga cikin mafi girman gagarimar matsalar ƙuncin rayuwar al’umma a duniya, inda aƙalla akwai mutum miliyan 8.7 a yankin masu tsananin buƙatar agajin gaggawa a cikin 2021.

“Kuma aƙalla akwai mutum miliyan 4.4 masu buƙatar abincin yau da na gobe, a yanayin da za a shiga na damina, kafin lokacin girbe amfanin gona ya yi.” Haka Ofishin Jakadancin Kasar Canada da ke Abuja ya bayyana.

Jakadan Riƙon Ofishin Jakadancin Canada a Najeriya, Nicolas Simard ne ya bayyana bayar da agajin maƙudan kuɗaɗen.

Sai dai kuma za ta bada kuɗaɗen ne ta hannun Cibiyoyin Ayyukan Agaji, irin su Majalisar Ɗinkin Duniya, Internarional Red Cross and Red Crescent Movement da wasu ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba.

Wannan tallafi dai Canada ta bayar da shi a matsayin cika alƙawarin da Kungiyar Mashahuran Ƙasashe 7 Masu Ƙarfin Tattalin Arziki na Duniya (G7) su ka ɗauka.

Ƙasashen G7 dai sun yi wani Tanadin Kandagarkin Ɓarkewar Yunwa Da Cututtuka a Yankin Arewa maso Gabas a Najeriya. A nan ne kowace ƙasa ta sha alwashin riƙa bada na ta tallafin da agajin.

Haka kuma ƙasar na aiwatar da tsarin ƙara bunƙasa rayuwar mata da ƙananan yara mata a cikin al’ummar da Boko Haram ya kassara.

A cikin shekarun 2019/2020, Canada ta kashe dala miliyan 123 wajen samar da agaji da jinƙai a Najeriya.

Najeriya ce ƙasa ta shida a duniya, a jerin ƙasashen da Canada ke bai wa agaji da jinƙai domin inganta rayuwar al’umma.

Share.

game da Author