Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta damke wani matashi mai shekaru 13 da ya kafta wa mahaifinsa Osariakhi Oronsaye adda cikin dare da adda.
Wannan dattijon, wanda shine mahaifin wannan yaro, mai shekaru 79 bai san hawa ba bai san sauka ba kawai sai ya ji an kafta masa kafceciyar adda yana barci da dare.
Wannan abun ban tausayin ya auku ne a Evbuotubu dake Benin City ranar Lahadin da ya gabata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kontongs Bello wanda ya sanar da haka ranar Litini a garin Benin ya ce babu wanda ke da masaniyar dalilin da ya sa wannan yaro ya aikata haka.
Kontongs ya ce rundunar za ta hada hannu da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na rundunar domin yin shawara da gudanar da bincike akai saboda yaron bai kai a kaishi kotu ba bisa dokar kasa.
Bayan haka Kontongs ya ce mazauna unguwan sun bayyana cewa a makon da ya gabata Oronsaye ya daure dansa a ofishin ‘yan saboda wani laifi da ya aikata.
Sai dai bayan ‘yan kwanaki Oronsaye ya sa an saki dan na sa.