Tiwita bai sanyawa Buhari takunkumi kamar yadda Trump ya bayyana cikin sakon sa ba – Binciken DUBAWA

0

Zargi: Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump a sakon taya murnar da ya aikawa Najeriya sakamakon badakalarta da Tiwita kwanan nan wai kamfanin ya sanyawa shugaba Muhammadu Buhari takunkumi

Ranar juma’a 4 ga watan Yunin 2021 gwamnatin Najeriya ta dakatar da duk huldudin kamfanin Tiwita a kasar na wani tsawon lokacin da ba ta fayyace ba, inda ta ce ana yawan amfani da dandalin wajen gudanar da ayyukan da ke barazana ga kasancewar Najeriya kasa daya dunkulalliya.

Wannan mataki na dakatar da dandalin sadarwar ya zo kwanaki kadan bayan da Tiwitar ta goge jawabin shugaba Muhammadu Buhari, inda ya yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa kan ofisoshin ‘yan sanda, gidajen yari, da ofisoshin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta INEC a yankin kudu maso gabashin kasar. Ya kuma kara da gargadin cewa duk wadanda ke goyon bayan tarzoma/tawaye da tashin hankali a kasar, “zai hukunta su da yaren/salon da suka fi ganewa”

Ga abun da jawabin ya ce: “Da yawa daga cikin wadanda ke wannan rashin hankalin yara ne wadanda basu da wayo sadda aka hallaka dukiyoyi da rayuka lokacin yakin basasar Najeriya. Mu da muka kasance a filin daga lokacin na tsawon watanni uku, muka kuma sha wahalar yaki, zamu hukunta su da yaren da suka fi ganewa”

Wadannan kalamai da shugaban kasar ya furta ya janyo martanoni iri-iri daga ‘yan Najeriya da ma al’ummar kasa da kasa.

Ranar talata 8 ga watan Yuni 2021, tsohon shugaban kasar Amurka, Donal Trump a wata sanarwa, ya taya Najeriya murna da ta dakatar da ayyukan Tiwita a kasar. Trump ya kuma yi kira da sauran kasashe da su bi sahun Najeriyar. Sannan ya ce tiwita ta sanyawa Muhammadu Buhari takunkumi.

“Ina taya kasar Najeriya murna bayan da ta dakatar da tiwita saboda sanyawa shugaban kasarta takunkumi. Ya kamata wasu kasashe ma su bi sahu su sanyawa tiwita da facebook takunkumi saboda sun hana mutane fadan albarkachin bakinsu – Ya kamata a baiwa kowane bangare murya. Yayin da wannan ke faruwa, sabbin kamfanonin sadarwar za su fito su fafata su kuma sami karfi. Ba su isa su gaya mana abun da yake dai-dai da wanda ba dai-dai ba tunda su kansu mugaye ne”

“Wata kila da abun da na yi ke nan da nake shugaban kasa. Amma Zuckerberg ya yi ta kira na a waya yana zuwa fadan shugaban kasa na White House muna cin bainci tare, har ma ya rika yaba mun yana cewa ina da kima a idon jama’a. 2024?”

Idan ba mu manta ba a watan Janairun 2021 Tiwita da Facebook sun sanya takunkumi kan shafukan Donald Trump sakamakon harin da aka kai kan Capitol Hill wanda shi ne mazaunin majalisun kasar. Kamfanonin biyu sun yi zargin cewa shi ya zuga ma’abotan shafukan shi su ka kai wannan harin da suka kai Capitol Hill saboda sakamakon zaben Nuwamban 2020 bai yi mi shi yadda ya ke so ba tunda ya sha kaye.

Tantancewa

Dubawa ta fara bincikenta da duba shafin shugaba Muhammadu Buhari (@MBuhari) dan ganin a zahiri ko shafin na nan ko kuma an soke, inda muka tabbatar shafin na nan ba abun da ya shafe shi.

Bacin haka ma, a wajen sanya takaitaccen bayani dangane da mai shafin, na Muhammadu Buharin ya bayyana shi a matsayinsa na shugaban kasan Najeriya har ma yana dauke da alamar tantance shafin da kamfanin twitar ke bayarwa.

A ranar laraba 9 ga watan Yuni, shafin na da ma’abota milliyan 4.1. haka nan kuma ranar 1 ga watan Yuni ne shugaban ya yi sharhinsa na karshe a shafi. Daga wannan ranar babu wani abu kuma. Sai dai bayan nan ne ya rubuta sharhin da kamfanin ya goge.

Manufofin kamfanin Tiwita na sanya takunkumi

Tiwita tana da wasu dokoki da manufofin da suke tabbatar da cewa kowa ya bada gudunmawa wajen tattauna batuwan da suka shafi al’umma cikin walwala da kwanciyar hankali.

Za’a iya sanyawa mai amfani da shafin tiwita takunkumi na dindindin idan har aka same shi da laifin ta’azara tashin hankali. Alal misali tiwita ta sanyawa tsohon shugaban Amurka Donald Trump takunkumi bayan da ya yi tsokacin da ya haddasa harin da aka kai majalisa wato Capitol Hill.

A sanarwar da ta baiwa manema labarai, inda ta bayyana dalilanta na sanya takunkumin ta ce “Bayan da muka tantance sharhunan da @realDonaldTrump ya yi da abun da suke nufi – musmman yadda jama’a ke fassara bayanan da ya bayar – mun goge shafin shi dindindin saboda maganganun shi a shafukan na iya fifita wutar tashin hankali.”

A cewar Tiwitar, idan aka cire shafin mutun daga manhajan tiwitar an cire shi ne dindindin ba yadda za’a iya maido shi ko da kuwa shi wane ne.

A wata hirar da ya yi da gidan talbijin na CNBC a Amurka, mai kula da harkokin kudin kamfanin, Ned Segal ya jaddada cewa dama can akwai “manufofin da aka tanadar dan hana jama’a tayar da tarzoma a shafin” kuma idan har sharhin mutun ya kunshi kalaman batanci za a goge.

“Idan har aka cire ka daga shafin an cire ka ke nan, ko da kai mai sharhi ne, ko mai kula da harkokin kudi ko ma dan siyasa na daa da na yanzu,” jami’in ya ce.

A lamarin shugaba Buhari ya karya dokar tiwita na “halin mugunta/keta” abun da ya kai ga goge sharhin da kuma dakatar da shafin shin a tsawon sa’o’i 12. Sai dai kafin a cire mutun daga shafin sai an kwatanta sakamakon karya wannan dokar da sauran dokokin da ka karya a baya. Wannan ne karon farko da Buhari ya yi amfani da irin wadannan kalaman a shafin.

Dan haka a wajen tiwita Buhari bai yi laifin da zai sa a cire shi baki daya daga shafin ba, shi ya sa basu yi haka ba.

A Karshe

Zargin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi ba gaskiya ba ne. Tiwita bai cire shafin Muhammadu Buhari ba. Tiwita goge jawabin da ya yi ne kawai wanda ya ce ya saba wa dokar kamfanin.

Share.

game da Author