Tun bayan tattaka fostan tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi a wajen taron jam’iyyar APC a Kano ranar dimokradiya, yan siyasa sun soki wannan abu da kakkausar murya suna masu cewa, Ganduje ya wuce gona da iri.
Da yawa daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu har da wasu makusantan gwamnan kan al’amarin sun bayyana rashin jin dadin su sannan sun ce Ganduje ya wuce ya rika nuna karanta irin haka.
Wani tsohon kwamishinan Ganduje, Abdullahi Mu’azu wanda aka dakatar dashi a baya kan wasu kalamai marasa dadi da yayi game da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nuna karanta ne abinda gwamnan jihar yayi a matsayin sa na shugaba kuma dattijo.
” Ko dai a banza shi Kwankwason ya taka muhimmiyar rawa har Ganduje yakai matsayin da yake a yanzu. Tare suke kaf a tsawon rayuwar siyasar su har ya kai ga darewa kujerar gwamnan jihar, amma mashawarta sun sa Ganduje ya nuna irin wannan ƙaranta a filin Allah Ta’ala saboda.
” Sannan kuma a matsayin sa na tsohon gwamna, tsohon Sanata, Tsonon mataimakin shugaban majalisa, Tsohon minista sannan a yanzu babu wani suna da ta ke da tasiri kamar sunan sa daga Kano a siyasar Najeriya, bai kamata Ganduje ya kankantar da kansa ba wajen aik abinda yayi a wajen taron ba.
Sai dai kuma wasu magoya bayan Gandujen sun ce basu ga wani abin tashin hankali akan abinda Ganduje yayi ba. Shi ma Kwankwason yaka tsakale shi saboda haka siyasa ce Ganduje yayi daidai.
Kwamishina yada Labarai na jihar Kano Mohammed Garba, ya bayyana cewa an yi wa bain da Ganduje yayi mummunar fahimta ne amma ba da gangar ya tattaka fostan Kwankwaso ba.
” A lokacin da gwamna Ganduje ya yi kokarin haurawa can sama yayi wa dandazon ‘ya’yan jam’iyyar APC jawabi, sai kuma a gefen sa akwai wasu ‘yan Kwankwasiyya da suka yi turuwa a wannan wuri za su canja sheka zuwa APC sai wasunsu suka rika jejjefa hotunan Kwankwaso a kasa shi kuma Ganduja ya murje su, amma ba da gangar bane.
” Wurin zuwa wajen yin jawabi ne Ganduje ya rika tattaka wadannan hotuna da aka watsa a kasa ba da gangar bani,shine ya sa aka lauya abinda don siyasa.
Jama’a da dama sun yi ta nuna rashin jin dadin su gane da abinda ya faru, inda suka ce Ido ba mudu bane amma ya san kima.
Discussion about this post