Soja ya harbe kansa bayan ya bindige wani ma’aikacin kwastam a iyakar Seme

0

Wani soja dake aiki a bataliya ta 243 a Ibereko Badagry LCP Mahmud Sulaiman ya bindige kansa har lahira bayan ya harbe wani kwastam.

Wannan abin tashin hankali ya auku ranar Laraba da karfe 7:45 na yamma yayin da shugaban sojojin dake aiki a shingen dake bodar Seme ke kokarin kwace bindigar daga hannu Sulaiman.

Shi shugaban sojojin ya nemi kwace bindigar saboda wasu halaye na rashin daya da hankali da Sulaiman ke nunawa.

Sai dai garin kokawar kwace bindigar, sai suka danna Karin, bindiga ko ta tashi, harsashi ya fice fut sai cikin wani jami’in kwastam C.N Walter dake tsaye yana kallon kwarauniyar.

Ganin haka kuwa ya faru sai Sulaiman shima ya dirka wa kansa harsashi nan take shima ya mutu.

An kai Walter babban asibitin Badagry amma ya rasu da safe da misalin karfe 6:40.

Kafin ya fara aiki a bodar Seme Sulaiman na aiki da dakarun sojojin dake yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya ne.

Sai dai tun da aka dawo da shi bodar Seme abokan aikinsa basu gane wasu haleyarsa ba.

Abokan aikin sun ce haka kawai Sulaiman sai ya rika loda bindigarsa kiran AK47 yana yawo da ita.

Ganin haka ya sa abokan aikinsa suka kai shi kara wajen kwamandan sojojin bataliya 234 Col. Nicholas Rume shi kuma ya bada umurnin a kwace bindigar daga hannun sa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar kwastam dake aiki a bodar Seme Abdulahi Hussiain ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari.

Share.

game da Author