Tsohon Ɗan Majalisar Jihar Nasarawa, Kassim Kassim ya bayyana cewa ba za su zuwa ido wasu tsiraru na yi wa Ali Modu Sheriff sharrin wai ya na ɗaukar nauyin ta’addanci ba.
Kassim ya ce a gaskiya jama’a na yi wa Sheriff rashin adalci matuƙar aka ci gaba da danganta shi da cewar ya na goyon bayan ta’addancin Boko Haram.
Kassim ɗan APC ne wanda ya ƙalubalanci rahoton da aka yaɗa, inda aka ruwaito wani Baturen Austaraliya mai suna Stephen Davies ya ce Sheriff ya na ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda.
Kassim ya ce Sheriff da kan sa ya sha ƙaeyatawa. Ya sha cewa da gaskiya ce zargin da ake yi masa, da tuni gwamnatin tarayya da ta jihar Barno sun fallasa shi.
Kassim ya ce abokan hamayyar siyasar sa ne kawai ke masa yarfe, domin a karya masa lagon ƙoƙarin sa na ciyar da APC gaba.
“Tun a ranar 10 Ga Disamba, 2004 fa Jami’an DSS su ka wanke Sheriff, su ka ce Stephen Davies sharri ya yi wa Modu Sheriff shi da tsohon Shugaban APC na Jihar Barno, Mala Usman.
Premium Times Hausa ta buga labarin cewa Sanata Ali Modu Sheriff na cikin ‘yan takarar shugaban jam’iyyar APC.
Ali Modu Sheriff ya shiga APC bayan kai ruwa rana da aka yi dashi a Jam’iyyar PDP, inda da kyar, da rokon Allah, fadi-tashi, da aka rika yi har da zuwa kotu kafinnan jam’iyyar PDP ta samu ya sauka daga kujerar shugabancin Jam’iyyar a 2016.