SALLAMA DA KORONA: Mutum 7 kacal suka kamu da Korona ranar Lahadi a Najeriya

0

Sakamakon gwajin cutar korona da aka fitar ranar Lahadi ya nuna cewa mutum bakwai ne kacal suka kamu da kwayoyin cutar korona daga jihohi uku a Najeriya.

Alkaluman sun nuna cewa mutum 8 ne suka kamu ranar Asabar sannan mutum bakwai a ranar Lahadi.

Bisa ga wannan sakamako wannan shine mafi kankanta da kasar ta samu tun bayan Afrilu 2020.

Hukumar NCDC ta ce jimlar yawan mutanen da suka kamu a Najeriya ya kai mutum 167,066 sannan babu Wanda aka rasa daga cutar daga ranar Lahadi zuwa kwanaki 10 da suka gabata.

Zuwa yanzu mutum 2,117 be suka mutu a dalilin kamuwa da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai cutar na ci gaba da yaduwa a bangarorin kasashen Asia da Kudancin Amurka.

Share.

game da Author