Garin rogo, wanda a ƙasar Hausa aka fi sani da garin kwaki, ya na ɗaya daga cikin abincin da duk wanda a shekarun baya aka ga ya daddage ya na ƙasumar sa, to ana danganta shi da talauci ko ƙarancin wadatar aljihu ko ta abinci a gida.
Amma a yau, duk da ɗimbin kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke kashewa wajen bunƙasa noma, hakan bai hana garin kwaki fecewa a guje ba, ya bi sahun sauran kayan abincin da ake nomawa a gida wajen tsula tsadar tsiya.
Kamar yadda shinkafa, wake, masara, gero da dawa su ke neman su gagari talaka, tuni shi garin rogo ya shige gaban su wajen tsada. Ya tsere wa gero da dawa da masara. Kuma ya yi wa talaka fintinkau, sai gani sai hange daga nesa.
Buhun garin kwaki mai nauyin kilo 100, wanda a shekarun baya ake sayarwa naira 16,000, yanzu idan ba ka da naira 40,000 ba za ta ka iya sayen sa ba a jihohi irin su Cross River, inda ake ganin kamar can ne ma ya fi arha takyaf.
Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna dalilai da dama da su ka haddasa ko da talaka ya iya sayen garin kwaki domin ya ci, to ba zai iya yi masa cin a ci a ƙoshi ba, irin wanda a shekarun baya ake tasa taiba a gaba ana ci har ciki ya cika.
Miliyoyin ma’aikatan da su ka ƙunshi na gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi waɗanda albashin su bai kai naira 40,000 ba, ba su iya cin garin kwaki su ƙoshi su da iyalan su. Sai dai a yi cin daga-bana-sai-baɗi, wanda ake yi ranar da aka ɗauki albashi.
Maciya tuwon alabo, wanda ake yi da rogo, su ma yanzu sai gani sai hange, ba kowa ke iya buɗe ciki ya danƙari tuwon alabo ba, duk kuwa da sulɓin ta lomar tuwon ke da shi. Saboda ba ta da sulɓi a cikin aljihun talaka.
A Najeriya dai batun tsadar abinci kullum sai hauhawa ya ke yi, ya ƙi saukowa ko gsngarowa ko kuma mirginowa a ƙasa.
A ƙididdigar da Hukumar Ƙididigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa ta yi a watan Afrilu, ta nuna cewa cikin watan Maris, 2021 kayan abinci a Najeriya sun yi tsadar da ba su taɓa yi a tsawon shekaru huɗu da su ka gabata ba.
Garin kwaki wanda shi ne aka fi nomawa na biyu daga masara a ƙasar nan, a yanzu bincike ya nuna wanda ake nomawa ɗin ba ya wadata.
Manoma irin su Grace Ebit da wasu masana sun danganta matsalar da rashin nahartaccen tsari da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa, rashin kyakkyawan tsarin noma, rashin jari ko rashin lamuni daga gwamnati da kuma ƙarancin taki.
Masana sun ce kafin rogo ya sake yin arha a Najeriya, sai an dasa aƙalla metrik tan miliyan 28.3 a filin gonakin da aƙalla sun kai faɗin hekta miliyan 1.2.
Cikin watan Mayu PREMIUM TIMES HAUSA ta yi tsskuren yadda wake ya fi ƙarfin tukunyar girkin manoman da ke noma shi.