Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana cewa za ta aika da jami’an tsaro makarantun sakandare m gwamnatin jihar guda biyar domin samar da tsaro.
Gwamnan jihar Inuwa Yahaya ya sanar da haka ranar Alhamis da ya ziyarci wasu makarantun sakandare mallakin gwamnati a jihar.
Makarantun da gwamnati za ta aika da jami’an tsaro sun hada da makarantar sakandaren kimiya da fasaha dake Dukku, makarantar sakandare na mata dake Doma, makarantar sakandaren Dadinkowa da makarantar Lakaje dake Kaltungo.
Yahaya ya ce gwamnati za ta inganta fannin ilimin jihar yadda dalibai za su rika samun ilimin boko fiye da kowace jihar a kasar nan.
Ya ce gwamnati na kokarin ganin kowace makarantar gwamnati ta dauki akalla dalibai 3,000 a jihar.
“Gwamnati ta za ta samar da ma’aikata da kayan aikin da za a bukata domin samar wa daliban ilimin boko ta gari.
Da yake duba aikin gyara da ake yi a makarantar Dadinkowa Yahaya ya ce gwamnatin sa a shirye take ta gyara makarantun jihar.
“Kafin yanzu makarantar Dadinkowa duk ta lalace.
Shugaban makarantar Saidu Aliyu ya jinjina aiyukkan inganta ilimin boko da gwamnati ke yi a jihar musamman a makarantar sa.
Aliyu ya ce tun da gwamnati ta fara gyara makarantar an samu karin yawan dalibai da ke shiga makarantar.
Discussion about this post