Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya kai ziyara jaje ga wasu garuwa da ke karamar hukumar Chikun wadand kuma suka yi iyaka da babban titin Kaduna zuwa Abuja.
El-Rufai ya ziyarci wadannan garuruwa ne bayan fama da suka yi da hare-haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Gwamna El-Rufai ya yada zango a garin Kakau inda ya zanta da mutanen garin.
Hakimin Kakau, Iliya Zarmai ya shaida wa gwamna El-Rufai cewa lallai suna cikin matsanancin hali a dalilin hare-haren ƴan bindiga da ya addabi mutanen garin.
Shi ko gwamna da ya yi wa mutanen Kakau jawabi ya ce tabbas gwamnati bata jin daɗin abinda ke faruwa a wannan gari da wasu sassan jihar Kaduna ba.
” Gwamnati na sane da abinda yake faruwa domin a kullum sai an kawo mata bayanan halin da tsaro yake jihar.
Daga nan sai kuma yayi gargaɗi ga mazauna garin Gonin Gora, su daina datse hanyar jama’a a duk lokacin da suke yin zanga-zanga a garin.
” Datse hanyar Abuja da mutanen Gonin Gora ke yi ba zai haifar da alkhairi ba sai da ma ya tunzura mutane da kuma zaman ɗar ɗar da fargaba. Sannan kuma an tauye wa matafiya damar su na yin tafi da ɓata musu lokaci.
Mutanen Gonin Gora sun datse hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Asabar da safe saboda hare-haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka addabe garin a cikin waɗannan kwanaki.
Wani mazauni ya bayyana cewa cikin mako guda ƴan bindiga sun sace mutane sama da 50 a garin.