RANAR KEKE TA DUNIYA: Tuka Keke zai rage farashin man fetur da inganta kiwon lafiya – Hukumar FRSC

0

Hukumar kiyaye haddura ta Kasa FRSC reshen jihar Kogi ta yi kira ga mutane da su rika tuka Keke domin rage yawan samun hadura a hanyoyin kasar nan.

Shugaban hukumar Solomon Agure ya sanar da haka a takardar da ke kunshe da jawabin sa na ranar tuka keke ta duniya da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a a Lokoja.

Taken taron bana shine ‘Tuka keke domin inganta lafiya’.

Agure ya ce keke na daya daga ababen hawa da ba a cika yawan samun hadari ba a kai.

“Keke na cikin ababen hawan da baya fitar da hayakin dake cutar da lafiya da muhalli kamar su mota, babura da sauran ababen hawa.

Ya ce har yanzu yana mamakin yadda babu shirin da gwamnati ta tsara da zai taimaka wajen wayar da kan mutane sanin mahimmancin tuka Keke a kasar nan.

Agure ya ce yawan amfani da ababen hawa dake amfani da man fetur na daga cikin matsalolin da ya sa ake fama da tsadar man fetur sannan da yawan cinkoso a hanya.

Ya ce a dalilin taron bana hukumar FRSC za ta shirya taro domin wayar da kan mutane sanin mahimmancin tuka keke sannan ma’aikatan hukumar za su rika tuka keke domin karfafa gwiwowin mutane su rika haka.

Agure ya yi kira ga direbobi da su kiyaye dokokin hanya sanna su guji tukin ganganci domin gujewa aukuwar hadari a hanyoyin kasar nan.

Yawan aukuwar hadarin ababen ya zama ruwan dare a kasar nan.

Bisa ga bayanan da FRSC ta fitar ya nuna cewa tukin ganganci da karya dokokin hanya na daga cikin dalilan dake kawo haka.

Share.

game da Author