RANAR CUTAR SIKILA TA DUNIYA: Duk shekara ana haifar jarirai 150 dake dauke da ciwon a Najeriya

0

A dalilin haihuwan jarirai 150 dake dauke da cutar a shekara Najeriya ta zama ƙasa da ta fi samun wadanda ake haihuwar masu dauke da ciwon Sikila.

Duk da haka gwamnatocin baya da na yanzu basu taka rawar gani ba wajen samar da kula, rage yaduwar cutar da wayar da kan mutane kan ciwon.
PREMIUMTIMES ta nemi karin bayani game da matakan da gwamnati ke dauke game da kawar da cutar daga kasar nan amma hakan bai yiwu ba.
An kebe ranar 19 ga Yuni na kowace shekara domin wayar da Kan mutane game da cutar sikila.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi haka ne domin wayar da kan mutane na cikin matakan dakile yaduwar cutar a duniya.

Ciwon Sikila a Najeriya

Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa akan haifi yara sama da 300,000 a duniya dauke da wannan ciwo.

Sannan kuma kashi 75 bisa 100 daga cikin wadannan yara daga kudu da Saharan Afrika suke, kashi 66 bisa 100 kuma daga Najeriya ake samun su.

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka (CDC) ta bayyana cewa akalla kashi 24 bisa 100 na mutanen Najeriya na dauke da wannan ciwo.
Sannan a duk jarirai 1,000 da ake haihuwa kashi 20 bisa 100 daga cikinsu na dauke da ciwon a kasar nan.

Yadda ya kamata a kula da mai dauke da ciwon sikila

Wata likita kuma shugaban gidauniyar ‘Sickle Cell Foundation Nigeria’ Annette Akinsete ta koka kan yadda ba a ba masu dauke da wannna cuta kyakkawar kula.

Akinsete tace a lokuta da dama likitoci kan yi kuskure wajen bada maganin karin jini wa mutumin dake fama da wannan cuta wanda hakan ke da mummunar hadari.

“Banda maganin rage radadin jiki da ake bai wa masu fama da ciwon kamata ya yi a rika ba shi Folic acid domin shine ke ke taimakawa jini a jiki.

Likitan ta kuma ce ya kamata a bai wa masu cutar sikila maganin kare su daga kamuwa da zazzabin cizon sauro wato ‘prophylaxis’.

Akinsete ta ce mai dauke da cutar ya rika shan ruwa ko kuma abinci mai ruwa ruwa domin guje wa bushewar jiki.

Share.

game da Author