RANAR BADA JINI TA DUNIYA: Kashi 27% na ‘yan Najeriya na bukatan karin jini duk shekara

0

Shugaban Hukumar lafiya ta duniya WHO na yankin Afirka, Matshidiso Moeti ta bayyana cewa akalla mutum miliyan bakwai ne ke bukatan karin jini a Nahiyar Afrika duk shekara.

Matshidiso ta ce a ƙasa Najeriya dake da mutane kusan miliyan 200 na bukatan jakan jini har miliyan 1.8 da za kara wa mutane duk shekara.

Ta ce zuwa yanzu kasar na maneji ne da jakan jini 500,000 a duk shekara.

Bisa ga takardun da ake shigarwa da wadanda ke fita kan bayanai bada jini na hukumar NBTS shugaban fannin shirye-shirye, bincike da lissafi Adaeze Oreh ta bayyana cewa daga shekarar 2019 zuwa 2020 hukumar ta samu jaka 25,000 na jini daga mutanen da suke bada jinin ba tare da an biya su kudi ba, wato kyauta.

“A takaice dai kashi 80% na jinin da hukumar ke samu na samuwa ne daga mutanen dake bada jini ga ‘yan uwansu dake bukata a asibiti.

Matsalolin da ake samu a dalilin rashin jini a Najeriya

Wani farfesa da ya kware a binciken jini kuma yake aiki da aikibitin koyarwa na jami’ar Legas LUTH Sulaiman Akanmu ya ce rashin samun isassun jini a asibiti daya ne daga cikin manyan matsalolin da ya sa ake yawan rasa mata musamman wajen haihuwa.

Ya ce a shekara Najeriya kan rasa mata 800 zuwa 840 daga cikin mata 100,000 dake zuwa asibiti haihuwa.

“Mafi yawan lokuta mace kan samu matsalar zuban jini bayan ta haihu sannan bisa ka’ida kamata ya yi a samu jinin da za a kara wa mace domin ta samu lafiya.

Sai dai kuma hakan ba shine ke faruwa ba.

Akanmu ya kuma ce akwai matsalar rashin jini da yara ‘yan ƙasa da shekara biyar kan yi fama da shi a dalilin cutar zazzabin cizon sauro.

Ya ce rashin samun jini a asibiti shima kan sa a fada cikin matsaloli da kan kai ga rasa ran maralafiya.

Matsalolin dake hana a samu jini a asibitoci

1. Rashin wayar da Kan mutane

Rashin wayar da kan mutane game da mahimmancin bada jini kyauta na da nasaba ne da rashin sani da canfe-canfen da mutane ke yi a kai.

2. Yawan siyar da jini

Wani sakamakon bincike da hukumar NBTS ta yi ya nuna cewa kashi 14% na mutanen Najeriya ba su bada jini sai dai idan fa za biya su ne idan suka bada.

Binciken ya kuma nuna cewa mafi yawan mutanen dake siyar da jini na yin haka ne saboda talauci, su sami kudin abinci.

3. Rashin isassun kudi a hukumar NBTS

4. Karancin wutar lantarki.

Wanda ya kamata ya bada jini.

1. Matasa masu shekaru 18 zuwa 65 za su iya bada jinin su bisa ga sharudan doka a Najeriya.

2. Mutumin dake da koshin lafiya zai iya bada jininsa sannan idan ya bada jinin zai ya jira har sai bayan tsawon kwanaki kafin ya sake bada jinin.

3. Mata za su iya bada jinin su amma mata musamman masu ciki, masu shayarwa, macen dake al’ada ba za su iya bada jini ba.

Share.

game da Author