Pillars ta ɗare saman Tebur bayan lallasa Eyimba da ta yi da ci 2-1 a Kano

0

Tun kafin a yi nisa da wasa, cikin minti takwas, Eyimba ta jefa kwallo ɗaya a ragar Kano Pilars.

Jefa wannan kwallo daya sai ya kara wa ƴan kwallon Pillars karfin guiwa, suka daɗa natsuwa sun taka leda.

Kan ace wani abu, Rabiu Ali ya rama wannan kwallo daya da aka saka a ragar Pillars, ta hanyar bugun daga kai sai gola bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Efeanyi Eze na Pillars da ya shi bayan an dawo hutun rabin lokaci ya mamayi Eyimba ya dirka kwallo ta biyu cikin ragar ta.

Daga nan fa sai Pillars suka tattare gida, ana da gumurzu har lokaci ya cika.

Wannan nasara da Pillars ta yi ya sa ta ɗare saman yebur din League.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka buga.

An buga wannan wasa babu Ahmed Musa wanda ya na can kasar Austria, wajen wasan kwallon kafa ta sada zumunta tsakanin Najeriya da Kamaru.

A wasan farko Najeriya ta saha kayi da ci ɗaya mai ban haushi. Za a yi arangama ta biyu ranar Talata.

Kano Pillars 2-1 Enyimba
Adamawa United 0-2 Plateau United
Kwara United 3-0 Jigawa Golden Stars
Abia Warriors 1-1 FC Ifeanyi Ubah
Dakkada FC 0-1 Lobi Stars
Wikki tourist 2-2 Akwa United
Heartland 2-2 Rivers United
Warri Wolves 2-1 Sunshine Stars
Katsina 2-1 Nasarawa United

Share.

game da Author