PDP za ta tsamo Najeriya daga dagwalon kwatamin da APC ta jefa ta -Tambuwal

0

Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana cewa gwamnonin Najeriya na ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun ƙudurci aniyar shiga gaba wajen tabbatar da cewa jam’iyyar su ta yi nasara a 2023, domin ceto Najeriya daga dagwalon kwatamin da ya ce mulkin jam’iyyar APC ys jefa ƙasar.

Tambuwal ya yi wannan furuci a Zauren Taro na Gidan Gwamnatin Jihar Akwa Ibom, a ranar Litinin, lokacin taron Gwamnonin PDP.

Ya ce ƙasar nan na buƙatar samun canji na haƙiƙa domin a canja waɗanda su ka fake da rigar canji su ka hau mulki, amma kuma su ka ƙara dulmiya Najeriya cikin rami gaba dubu.

Ya ce da yardar Allah PDP ba za ta bai wa Najeriya kunya ba.

Sannan kuma ya nemi a ci gaba da jajircewa da yin addu’o’i, domin matsalar da aka jefa ƙasar nan a cikin ta, na buƙatar ɗauki daga ɓangsrori daban-daban.

Har ila yau, a wurin taron, Gwamnonin PDP sun bayyana cewa Gwamnatin APC ta maida NNPC kandami a sha a yi wanka, CBN ya koma rijiyar tsakiyar gari, wadda kowa ke jefa gugar sa ya kamfaci ruwa yadda ya ishe shi.

A wani sabon zargin yadda ake ta kamfata da jidar kuɗaɗe a ƙarƙashin gwamnantin APC, Ƙungiyar Gwamnonin PDP sun bayyana cewa manyan hukumomin tara kuɗaɗen gwamnatin tarayya sun zama wuraren da a kullum a ke ta yi wa dabdala da rubdugun wawurar kuɗaɗe.

A taron da gwamnonin na APC su ka yi a Uyo babban birnin Akwa Ibom, gwamnonin na PDP sun nuna fushin yadda kamfanin NNPC ya zama babban kandamin a sha a yi wanka, wanda gwamnatin APC ke kamfatar maƙudan kuɗaɗe kai-tsaye ba tare da bin tsarin federaliyya wanda dokar Najeriya ta gindaya ba.

Sun kuma bayyana cewa tuni Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tashi daga bankin ‘yan Najeriya, ya koma rumbun watandar jami’an gwamnatin Buhari.

Sauran hukumomin da Gwamnonin PDP su ka zarga ana amfani da su a ƙarƙashin gwamnantin APC ana nuna bambanci da son rai ana talauta ‘yan Najeriya, sun haɗa da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), NIMASA, NCC, Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS) da kuma Hukumar Kwastan ta Ƙasa

Sun bada misali da yadda NNPC ke kashe kuɗaɗen fetur duk yadda ta ga dama, a lokacin da ta ga dama, ga wanda ta ga dama kuma ko nawa ta ga dama.

Gwamnonin sun tunatar yadda watan Afrilu NNPC ya ƙi bai wa Gwamnatin Najeriya ko sisi daga kuɗaɗen da ya kamata ta bayar daga cinikin fetur, domin a raba wa Tarayya, Ƙananan Hukumomi da Jihohi.

Wannan mummunan hukuncin karya doka inji PDP, ya tauye wa ‘yan Najeriya kuɗaɗen da suka kamata a yi masu ayyukan bunƙasa ƙasa.

CBN Ya Zama ‘Yar-rototuwar Da Ke Wa Gwamnatin APC Aman Kuɗi Su Na Lashewa -Gwamnonin PDP

“Shi kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zama ‘yar-rototuwar da ke wa gwamnatin APC aman kuɗi su na lashewa a lokacin da su ke so.

“CBN ya zama babu mai sa masa ido ko mai hana bankin duk abin da ya ga damar yi. Domin ta kai har ya na buga kuɗaɗe yadda ya ga dama, ya yi abin da ya ga dama da kuɗaɗen kuma ya kashe duk abin da ya ke son kashewa, ba tare da ana yi masa linzami ba.”

A ƙarshe gwamnonin waɗanda a taron, har da Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, sun yi kira ga bankunan Najeriya da su taimaka su ceto naira daga karyewar da darajar ta ke yi a dullum wayewar gari.

Share.

game da Author