Ba girman ka ba ne ka rika rinton ayyukan da ba kai ka fara su ba

0

Jam’iyyar PDP ta zargi Shugaba Muhammadu Buhari da rinton ayyukan raya kasar da ba gwamnatin sa ta kirkiro ba, ba shi ya aza harsashen su ba, kuma ba shi ya fara gina su ba.

PDP ta bakin Kakakin Yada Labarai Kola Ologbondiyan, ya ce wasu ayyukan da Buhari ke dukan kirjin ya yi, duk ayyukan da PDP ta fara ne, amma ba a kammala ba.

Ya ce yawancin ayyukan da Buhari ya rika cewa shi ya yi su, duk ayyukan da gwamnatocin PDP a zamanin Obasanjo, Yar’Adua ko kuma Goodluck Jonathan aka fara su, ko aka kammala ko aka kusa kammala su.

PDP ta yi wannan zargi ne bayan wata tattauanawa da Arise TV ta yi da Buhari, wadda aka nuna a ranar Alhamis, inda Buhari ya rika bayanin wasu nasarorin da ya ce gwamnatin sa ta samar.

“Haba jama’a ai ba girman Shugaban Kasa ba ne ya rika fitowa kiri-kiri a gidan talbijin ya na rinton ayyukan da ba shi ya yi ba. Kuma kowa na kallon sa.”

Yayin da jama’a da dama ke yaba kokarin Gwamnatin Buhari a tsawon shekaru shida kan mulki, PDP ta ce babu wani nagari ga abu doyi, domin gwamnatin Buhari ta gaza ta kowane fanni.

“Idan Buhari bai sani ba, to bari mu sanar da shi ayyukan da ya ke ta karkarwar cewa shi ya assasa su, ba gaskiya ba ne, gwamnatin PDP ce ta fara kirkirowa da assasawa da fara ayyukan fadada manyan titina a kasar nan, titinan jiragen kasa, da sauran wadanda hadiman sa su ka nunke shi baibai, su ka ce duk shi ne ya kirkiro su.

“Kowa ya San Shugaba Jonathan ya yi gagarimin aikin fadada titinan jiragen sama da su kan su filayen jiragen sama din. Kuma ya gina tashoshin jiragen kasa har ma ya kaddamar da wasu.” Inji PDP.

Share.

game da Author