‘Obama na Amurka da bashi yayi karatu, akwai hanyoyin cin bashi muma a nan, ba za mu janye karin kudin makaratar jami’ar Kaduna ba – Gwamnatin Kaduna

0

Gwamnatin Kaduna ta gana da wakilan Daliban Jami’ar KASU, ba za a janye karin kudin makaranta ba

Gwamnatin Jihar Kaduna gana da wakilan daliban Jami’ar ranar Alhamis, inda ta shaida musu cewa sai dai fa su yi hakuri amma maganar rage kudin makaranta an wuce nan, gwamnati ba za ta janye karin kudin makaranta da ta yi ba.

Mataimakiyar gwamnan Kaduna, Hadiza Balarabe, ce ta jagorance tawagar gwamnatin, wanda bayan ita akwai sakataren gwamnatin jihar Balarabe Lawal, da shugaban Ma’aikatan fadar shugaban gwamnatin jihar, Mohammed Abdullahi.

A jawabin da yayi wa wakilan daliban, sakatare Balarabe yace kudin da ake biya kafin a kara yayi kadan matuka. ” Akwai makarantun firamare a Kaduna da ake biyan kudin makaranta har naira ₦100,000, haka kuma akwai wadanda ake biya har naira ₦500,000 karatun sakandare sannan ace wai karatun jami’a naira ₦26,000.

Ita ko mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe, cewa ta yi kudin makarantar da dalibai ke biya ba ya iya biyan albashin malaman jami’ar ballantana wai ace za a yi wani aiki da shi.

Sai dai kuma su wakilan daliban sun roki gwamnati ta tausaya wa talakawa wanda sune suka yawa a jami’ar a rage mudin ko da rabi ne domin su iya biya.

” Bukatar mu shine gwamnati ta tausaya mana, ta rage kudin makarantar koda rabi ne, domin a gaskiya karin zai gurgunta karatun wasu da dama daga cikin daliban Jami’ar.

A karshe gwamnati ta dai sanar da daliban cewa ba fa za ta janye ko ta rage kudin makarantar ba, amma akwai hukumar bada tallafin karatu na jihar Kaduna, dalibai su garzaya don neman tallafi, ko kuma su nemi bashi su yi Karatu.

” Obama na Kasara Amurka ma da bashi yayi, karatu, idan baka da kudi za ka iya cin bashi ka yi karatu”.

Share.

game da Author