Najeriya za ta sayar wa kasashe hudu wutar lantarki ‘wadda ba ta bukata’

0

Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirye-shiryen sayar da wutar lantarki ga kasashe hudu na Afrika ta Yamma.

Kasashen sun hada da Togo, Burkina Faso, Benin da Nijar, kamar yadda Shugaban Riko Kamfanin Raba Wuta (TCN) da Shugaban WAPP Sule Abdulaziz ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba.

“Karfin hasken lantarkin da za mu sayar wa wadannan kasashe shi ne wanda ba a bukata a nan Najeriya.”

Hausawa dai na cewa “idan kura na maganin zawo, to ta fara yi wa kan ta.”

Najeriya, kasar da ta shafe kusan shekaru 30 cikin matsalar wutar lantarki, ita ce ke sanar da cewa za ta sayar da wutar da ba a bukata a nan kasar.

Binciken PREMIUM TIMES ya nuna cewa hatta babban birnin Tarayya Abuja, a cikin matsananciyar matsalar rashin wuta ya ke kusan makonni uku kenan.

Abdulaziz ya ce Najeriya za ta ci moriyar shirin ta hanyar samun kudaden shiga da kuma samar da aikin yi.

“Idan aka kulla wadannan cinikayya da kasashen hudu, Najeriya za ta samu kudaden shiga masu yawa. Kuma ‘yan Najeriya za su samu aikin yi sosai.” Cewar Abdulaziz.

Ya kara da cewa kasashen hudu za su sayi wutar ce daga layukan Raba Wuta na North Core Power Transmission Line da ake aikin sa kan dala miliyan 570.

Aikin dai Bankin Duniya da Majalisar Bunkasa Fransa da bankin AfDB su ka bayar da ramcen kudaden aiki.

Za a kammala aikin nan da shekaru biyu.

Share.

game da Author