Najeriya ta fi yawan yaran da basu makarantar boko a Kudu da Saharan Afrika – Minista

0

Karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana cewa Najeriya ta fi yawan yaran dake gararamba basu makarantar boko ba a kasashen dake yankin Kudu da Saharan Afrika.

Nwajiuba ya fadi haka ne a taron kadamar da shirin samar da ilimin boko ga kowa da kowa BESDA da aka yi a jihar Katsina ranar Litini.

A lissafe dai yara akalla miliyan 10,193,918 neba su makarantar boko ba a Najeriya.

Ya ce rashin ware wa fannin kudade, rashin isassun malamai, rashin kayan aiki na daga cikin matsalolin dake hana yara samun ilimin boko a kasar nan.

Nwajiuba ya jinjina namijin kokarin da gwamnan jihar Aminu Masari ke yi wajen farfado da fannin ilimin boko a jihar.

Ya ce yin haka da gwamna Masari ya ke yi tabbatar da shugabancin na gari ne da mika kai wajen ganin mutanen jihar sun samu ilimin boko kamar yadda kowa ke samu.

Nwajiuba ya ce shirin BESDA na aiki a jihohi 17 a kasar nan.

Ya ce daga cikin jihohi 17 da shirin ke aiki a kasar nan 13 daga ciki su na yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas sannan da jihohin Niger, Oyo, Ebonyi da Rivers.

A nashi jawabin Masari ya yaba wa shirin inganta fannin ilimi da hukumar UBEC da ma’aikatar ilimi ke yi a kasar nan.

Share.

game da Author