Gwamnonin jam’iyyar PDP na can garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom suna ganawar yadda za su kwace mulki daga jam’iyyar APC mulki ta dawo musu.
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun gaji APC yanzu Allah-Allah suke 2023 yayi su kora su gida.
Tambuwal ya ce PDP ba zata ba ƴan Najeriya kunya ba ganin yadda suka raja’a gaba ɗaya akan jam’iyyar domin ta samo musu mafita.
” Ga jaruman ku nan, gogaggu, fitattu, dakarun ku kuma gwamnonin ku wadanda ku ne a gaban su, tare da mu da ku da addu’o’in da zaku yi mana, za mu yi nasarar ceto Najeriya daga halin da ta shiga.
” Muna sa ran in Allah ya yarda, za mu kwato mulki, zata dawo wajen mu, jam’iyyar PDP, a 2023.
A karshe ya roki ƴan Najeriya su dage da addu’o’i somin a samu kasa ta fito daga cikin matsalolin da ya kannannaɗeta.
A nashi jawabin a wajen taron gwamnan Akwa Ibom Emmanuel Udom ya yabawa gwamnatocin kan yadda suka jajirce wajen yi wa mutanen su da al’ummar aiki tukuru domin cigaban su da jihohin su baki da.
Jam’iyyar PDP na ci gaba da ganawa a tsaknin au da kuma neman sulhu a tsakanin su musamman ga wadanda ba a yi daidai ba domin a dawo a dunkule ya karbo mulki daga APC a 2023.
Discussion about this post