Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna damuwar sa dangane da wata sabuwar barazana da ‘yan ta-kifen Neja Delta su ka ayyana barazanar ƙaddamarwa a yankin.
‘Yan ta-kifen masu suna Niger Delta Avengers, sun yi barazanar fara kai hare-haren durƙusar da tattalin arzikin Najeriya.
Wata sanarwar da aka danganta cewa ta fito daga hannun su, ta ce za su fara kai hare-haren hare-hare a kan masana’antun haƙo mai da kuma sauran kadarorin gwamnatin tarayya da ke yankin.
Sannan kuma sun yi barazanar kai hare-hare kan ‘yan siyasar yankin na su, masu haɗa kai da gwamnatin tarayya.
Sai dai kuma wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Adesina ya sa wa hannu, ta bayyana cewa Shugaba Buhari ya cika da mamakin wannan kalami na rashin godiyar Alaihi da ya fito daga bakin ‘Yan Ta-kifen.
Ya ce ya yi mamakin yadda su ka yi wannan kalami ƙasa da sa’o’i 48 da Shugaba Buhari ya gana da Shugabannin Yankin Neja Delta da kuma ‘yan Ijaw National Congress a fadar sa.
Ya ƙara da cewa a tattaunawar Buhari ya umarci Ministan Muhalli ya gaggauta aiwatar da aikin kwashe dagwalon ma’asanantun gurɓataccen ɗanyen mai da ya lalata yankuna da dama na yankin na Neja Delta.
Kuma ya bada umarnin cewa duk inda za a yi aikin, a ɗauki matasan yankin a yi aikin da su.
Batun neman ƙarin samar da Jihohi biyu da ƙarin Ƙananan Hukumomi a yankin kuwa, Buhari ya ce wannan magana ce ta Majalisar Dattawa da ta Tarayya, su ne ke da wuƙa da nama.
Haka ma batun sake fasalin Najeriya da su ka nema, Buhari ya ce duk magana ce ta Majalisar Dattawa.
“Ni dai duk abin da su ka zartas, idan ya zo kan teburi na ba zan ɓata lokaci ba zan sa masa hannun amincewa.”
Haka Buhari ya ce batun aikin Babban titin da ya haɗe Yankin Gabas da Yamma, wanda zai karaɗe jihohin Neja Delta ya haɗe su da Kudu maso Gabas, duk ya na a ƙarƙashin ajandar sa.