Mutuwar TB Joshua: Kiristoci sun yi baban rashi a kasar nan – Mabiya

0

Mabiya Cocin Synagogue dake Legas sun yi tururuwa a cocin ranar Lahadi suna ta koke-koke da jimamin rasuwar babban Faston Cocin Synagogue, TB Joshua wanda ya rasu ranar Asabar.

Masu ibada sun yi tururuwa zuwa cocin da safiyar Lahadi. Wasu da dama basu yarda faston ya rasu ba, suna ta kuka suna ba zai yiwu ace kamar sa ya rasu ba.

” ” Inaa, Fasto TB Joshua bai rasu ba, yana nan, ni dai ban yarda ya rasu ba. Ku daina ce min ya rasu”. Haka wata mabiyar sa ta rika fadi a harabar Cocin dake jihar Legas ranar Lahadi.

Cikin wadanda suka aika da sakon ta’aziyyar su ga iyalan marigayin harda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda ya yi alhinin rasuwar faston sannan kuma ya mika gaisuwarsa ga iyalan mamacin da sauran kiristocin Najeriya.

Marigayi TB Joshua yayi suna matuka wajen aikin wa’azi da kuma warkar da marasa lafiya ta hanyar addu’o’i a coci. Yana daga cikin manyan fastoci a kasar nan da suka yi fice kuma suke da mabiya ba a Najeriya ba harda kasashen dake makwabtaka da Najeriya.

Share.

game da Author