Idan ba a manta ba a ranar Litini ne hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa Najeriya ta fara yin sallama da yaduwar cutar korona inda a ranar Lahadi alkamunan yaduwar cutar suka nuna cewa babu wanda ya kamu da cutar.
Alkaluman sun kara nuna cewa Najeriya ta yi tsawon makonni biyu ba tare da cutar ta kashe wani ba.
Sai dai murna ta koma ciki ranar Litini bayan bayyana sakamakon gwajin cutar da NCDC ta yi wanda ya bayyana cewa mutum 86 sun kamu sannan mutum daya ya mutu a kasar nan.
Mutum 52 sun kamu a jihar Legas, Ondo – 31 da Akwa Ibom – 3.
Gwamnati ta yi wa mutum 2,266,591 gwajin cutar daga cikin mutum miliyan 200 dake zama a kasar nan.
Mutum 163,797 sun warke sai dai har yanzu akwai mutum 1,500 dake killace a asibiti.
A kwanakin da suka gabata Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa gwamnati za ta karbi karin kwalaben maganin rigakafin Korona na Oxford-AstraZeneca daga asusun COVAX.
Shu’aib ya ce Najeriya na sa ran karbar kwalaben maganin a karshen watan Yuni ko kuma a watan Agusta.
Hukumar NPHCDA ta bayyana cewa mutum 1,978,808 ne suka bada kansu domin allurar rigakafin korona zangon farko a kasar nan.
Sannan a zango na biyu mutum 680,345 suka yi allurar rigakafin korona a kasar nan.
Shu’aib ya yi kira ga wadanda suka yi allurar rigakafin korona zangon farko da su gaggauta zuwa domin yin allurar zango na biyu.